Idan ka tashi neman aure, ka yi shawara da manya. Saboda sun rayu a jiya, sun kuma ga goben da ba ka ga ba (rayuwa da iyali). Kar ka biye wa son zuciyarka, mai nema da ɗaukar shawara ba ya nadama.
Dattijo ya mana nasihohi 10 masu tsada kan neman aure:
1. Idan ka tashi neman matar aure, kada ka duba kyau, ka duba ɗabi'a.
Mata masu kyau (wasu) a zamanin nan, idan za su aure ka gani suke (kamar) alfarma za su ma saboda yawan manema. Ɗabi'a ita ce ke zaunar da mutum a gidan aure. Ida ka dace ka haɗa kyau da ɗabi'a.
2. Ka nemi gidan da suke daidai da wadatarka ko waɗanda (kai) ka fi su wadata, za su ƙimanta ka.
Idan ka nemi gidan da suka fi ƙarfin tattalinka, (wasu) za su raina arziƙinka, da abin da za ka kai musu. Za kuma suna ga kamar alfarma ma suka maka.
3. Idan ka tashi aure, ka auri wacce take sonka. Kar ka kuskura kuɗi (kaɗai) ne zai ma aure. Ko a 'latecomer' ka je, ka fara neman soyayya, kada ka yi ƙarfafa neman aure musamman a zamanin nan.
4. Mata da yawa kalar iyayensu mata ne. Suna tasirantuwa matuƙa da iyayensu mata. Haka kai ma 'ya'yanka za su tashi. Ka kiyaye auren mai kisisina ko zuwa wajen bokaye.
5. Ka kiyayi mace mai dogon buri. Za kana iya bakin ƙoƙarinka tana rainawa. Wata (ma) ta jefa ka cikin masifar cin basussuka don biya mata buƙatun da ba dole ba.
6. Kar ka yi ƙarya a wajen aure. Zaman aure zahiri ne, idan aka tarar da saɓanin yadda ka bayyana, raini ne zai biyo baya.
7. Ko kyauta za a ba ka aure, kar ka kuskura ka yi aure ba ka da sana'a ko wadatar riƙe iyali. Eh! Allah ne ke ciyarwa, amma ba a irin wawan tunaninka ba, ba ka nema ba, kana tunanin kana zaune arziƙi zai faɗo daga sama?
8. Ka yi niyyar aure don ibada, ba don gasa ba, ko gusar da sha'awa ba kaɗai.
9. Kana shawara da manyanka, musamman mahaifi, mai shawara ba ya nadama.
10. Ka dage da addu'a, ka nemi zaɓin alheri daga Allah.
#AliyuMAhmad #RayuwaDaNazari
#AliMotives #NemanAure
0 Comments