Bacin Rai da Damuwa

Ɓacin rai da damuwa na ɗan lokaci ne. Abin da ya sa muke ɗaukar lokaci cikin ɓacin rai ko damuwa, mu yi masa ban ruwa ne da yawan tunani.

Yawan tunani kan abin da ya sabbaba ma damuwa, misali cin amana, ko rashin wani masoyi (mutuwa), cin fuska, cusgunawa da sauransu, ba zai rage ma damuwa ba, sai dai kullum ka ci gaba da dauwama cikin damuwar, saboda kamar kana mata ban ruwa ne.

Yawan damuwa yana daga cikin abin dake ragewa jiki kuzari (enerygy). Wannan ya sa, sau da yawa idan wani na cikin damuwa yake ramewa, a lokacin da (kuma) ya sanu kwanciyar hankali da nutsuwa yake haske, kuzari da ƙiba.

Maimakon ka zauna kana ta tunani kan damuwa, ka shagaltar da kanka da maimaita 'ASTAGHFIRULLAH' (a kullum), a hankali zai maye gurbin yawan tunani, a hankali damuwarka za ta kau.

#AliyuMAhmad #RayuwaDaNazari #AliMotives

Post a Comment

0 Comments