#Matashi
Ba don matasa na ɓata lokacin biya 'yan mata da soyayya ba, da rayuwar matasa da yawa tafi haka samun ci gaba.
Idan ka yi nazari cikin abokanka da suka tattala jari, suka mallaki gida, suka yi aure, suna cikin rukunin waɗanda ba sa ɓata rayuwarsu wajen tara 'yan mata, har ka ji ana cewa "wane da ya yi aure, da ba ruwansa da harkar soyayya, ashe tanadi yake...".
• A lokacin da kake kashe kuɗin sa 'airtime', biyan kuɗin anko, farantawa ƙauna..., a lokacin yana tattala nasa.
• A lokacin da kake doguwar waya, hira, ko chats..., a lokacin yana karatu ko yana wajen sana'arsa (ya maida hankali waje ɗaya).
• A lokacin da kake baƙin cikin 'heartbreak', yana bacci da munshari, ba shi da damuwar kowa.
• A lokacin da ka 'breakup' da 'BARIRA', kana ƙoƙarin 'crush' a kan 'SHAMSIYYA', shi kuwa yana ƙoƙarin investing sabon business.
Soyayya da ba ka shirya AURE ba, ƁATA LOKACI ce. Lokacinka, lafiyar kwakwalwarka, kuɗinka... suna muhimmancin tattalawa. Kar biye sha'awa, kuruciya da son zuciya.
#AliyuMAhmad #RayuwaDaNazari #AliMotives
0 Comments