Mentor a Social Media


Mentor daban
Influencer daban
Role model daban
Coach daban

• MENTOR - shi ne wanda ka ƙulla alaƙa da shi don ya riƙa ba ka shawarwari kan wani ɓangare na al'amuran rayuwarka na tsawon lokaci. Misalin alaƙar Salisu Abdurrazak Saheel (mantee) da Professor Isa Ali Pantami (mentor).

• INFLUENCER - shi ne wanda kake tasirantuwa da shi ta hanyar rubutunsa/wallafa, maganarsa ko wani abu da yake gabatarwa na basira ko kwarewa. Misali, Badamasi Aliyu Abdullahi (kan kasuwanci), Aliyu M. Ahmad (kan rayuwa da fasahar zamani), Anas Darazo da Zoohrah Oummu Deederht (zamantakewa) da sauransu.

• ROLE MODEL - shi ne wanda ya kake son zama kamarsa, har kake kwaikwayon irin tsari da salon rayuwarsa. Misali, wani babban ɗan siyasa, malami, ko shararren mutum.

• COACH - shi ne wanda zai 'guiding' ka daga farko har tuƙewa kan lamuranka na ɗan lokaci (kamar a a wani 'skills', kwallo, ko wani 'program').

* Ana kuma iya samun dukkan siffofi ko wasu a mutum ɗaya.

Abin da ya sa na ce samun 'MENTOR' yana da sauƙi sosai a 'SOCIAL MEDIA', misalin kwararrun mutanen da suke buɗe ajujuwan koyar da 'skills', da zarar ka yi joining classes ɗinsu ka ƙulla alaƙa da 'mentor'. A taƙaice, malaminka 'coach' ɗinka a lokacin 'program', sannan kuma 'mentor' ɗinka ne idan kun ci gaba da alaƙa har tsawon rayuwarka.

Akwai waɗanda suka sami 'mentors' kan scholarship a social media, yanzu haka suna ƙasashen wajen karatu da 100% na tallafin karantu. Ka bibiyi Yakubu Sani Wudil ko AREWA YOUTH MENTORSHIP PROGRAM da sauransu.

Kuma kamar mu a ajinmu na 'SOCIAL MEDIA MANAGEMENT' da 'CONTENT CREATION', a lokacin darasi ana 'coaching' da 'mentoring'. Bayan darasi kuma ana ci gaba da 'mentoring', saboda ko wani project mutum zai yi, zai iya tuntuɓarka shawara. Misali, 'influencer' kamar Badamasi Aliyu Abdullahi zai zama 'mentor' ɗinka ne idan kun ƙulla alaƙar neman shawararin kasuwanci, kuma 'BDSP' ne. Haka Ouumu Deederht kan alaƙar aure ko soyayya. Da yawa, 'MENTORSHIP' a Arewa 'FREE' ne, wuyarta ka ƙulla alaƙar.

#AliyuMAhmad #RayuwaDaNazari #AliMotives
#Mentor #Mentorship #Coach #Influencer

Post a Comment

0 Comments