Laƙani


Ka karanta kafin ka yi bacci:

Idan kana da wani laifi (mai jaraba) da ka kasa dainawa na alfasha kamar zina, kallon batsa, shaye-shaye..., ko yawan damuwa, ko kuma kana neman kusanci ko wata buƙata a wajen Allah ﷻ, zan ba ka wani laƙani guda 3 na tsawon kwana 40;

1. KIYAYE SALLOLIN FARILLA DA YAWAITA ZIKIRI

A cikin Alƙur'ani, Al-anƙabut aya ta 45, Ubangiji ﷻ yana cewa: "وأقم الصلاة إن الصلاة تنهى عن الفحشاء والمنكر ولذكر الله أكبر". Ma'ana, "Kuma ka tsaida sallah, lalle salla tana hanawa daga alfasha da abin ƙyama (na laifi), kuma lalle ambaton Allah yafi girma, Allah ya sane da abin da kuke aikatawa".

Ya tabbata a hadisin Tirmidhi (241), Anas bin Malik رضي الله عنه ya ce, Manzon Allah ﷺ ya ambata cewa, "من صلى لله أربعين يوماً في جماعة يدرك التكبيرة الأولى كتبت له براءتان براءة من النار وبراءة من النفاق "

Ma'ana, "duk wanda ya kiyaye sallah ta kwana arba'in (a jere, daga Asuba, Azahar, La'asar, Magriba da Isha'i) yana mai riskar kabbarar farko (takbiratul ihram), za a kuɓutar da shi daga wuta da kuma munafurci". (Ya kasance sallar a jam'i ce, kuma kana ƙoƙarin ana tada sallah tare da kai na tsawon kwana 40, za ka yadda rayuwarka za ta sauya).

Yawaita zikiri, ka kiyaye:

• Yawaita karatu ko sauraron Alƙur'ani,
• Zikiran tashi da kwanciyar bacci,
• Zikiran sunnah na safiya da maraice, 
• Zikiran ciki da na bayan sallah,
• Zikiran gudanar da al'amuran yau-da-kullum, kamar sanya wa da cire tufafi, shiga da fita daga gida; zuwa, shiga da fita daga masallachi, hawa abin hawa, shiga kasuwa, tashi daga wurin aiki ko majalissi...
• Yawaita Istighfari,
• Yawaita salatin Manzon Allah ﷺ. 
• Yawaita Albaƙiyatus salihaat (hailala, tasbihi, tahlili, tahmidi) ba adadi.
• Yawaita addu'o'in alheri da neman biyan buƙata.

2. KIYAYE NAFILOLI

A cikin Bukhari (6502), hadisin Abu Hurairah رضي الله عنه, hadisin Ƙudsi, Manzon Allah ﷺ yana cewa, Ubangiji ﷻ na cewa: "وما يزال عبدي يتقرب إلي بالنوافل حتى أحبه ، فإذا أحببته كنت سمعه الذي يسمع به ، وبصره الذي يبصر به ، ويده التي يبطش بها ، ورجله التي يمشي بها ، وإن سألني لأعطينه ، ولئن استعاذني لأعيذنه". 

Ma'ana, "Bawana ba zai gushe ba yana neman kusanci da ni da nafiloli ba har sai na so shi. Idan na so shi, zan kasance jinsa da yake ji da shi, ga ganin da yake gani da shi, hannunsa da yake jimka (taɓa wani abu) da shi, da kuma kafafuwansa da yake tafiya da su (ma'ana zai na kiyaye gaɓɓansa na gani, ji, taɓawa da tafiya sai ga iya abin da Allah yake so). Kuma idan (bawan) ya roƙe ni (in ji Ubangiji), sai na ba shi, kuma idan ya nemi tsarina, sai na tsare shi".

Daga cikin nafilolin sallah da za ka kiyaye, akwai:

• Raka'o'i 2 bayan fitowar alfijir
• Sallar wahala, daga raka'a 2, 4 ko 8 bayan ɗagowar rana zuwa zawali (kamar 7:30am zuwa 12:00pm),
• Raka'o'i 4 kafin sallar Azahar, 2 bayanta,
• Raka'o'i 2 kafin sallar La'asar,
• Raka'o'i 2 bayan sallar Magriba,
• Raka'o'i 2 kafin sallar Isha'i, da 2 bayanta,
• Shafa'i da wuturi,
• Tahajjud (sallah/tsayuwar dare) daga raka'a 2 zuwa sama,
• Tahiyyatul Masjid raka'a 2 a duk lokacin da ka shiga masallaci.

Daga cikin nafilolin azumi, akwai:

• Azumin Litinin da Alhamis,
• Azumin Annabi Dauda, idan za ka iya, yau yi, gobe ka sha,
• Azumin Sittu Shawwal,
• Azumin ranar Arfa,
• Azumin Ashura da Tasu'a,
• Ayyamu al-bid, azumin nafila a ranakun 13th, 14th da 15th na watannin Hijira,
• Yawaita azumin nafila a watan Rajab.

Daga cikin sadaka ta nafila, akwai ciyarwa, tufatarwa, ilmantarwa, hana ɓarna, kawar da abu mai cutarwa a kan hanya da sauransu.

3. NESANTAR WURAREN SAƁO DA KUSANTAR MAJALISSAN KARATU DA MUTANEN KIRKI

Dole ne idan kana son sauya wasu ɗabi'u sai ka dai zuwa wurin da ake wannan alfashar, sannan ka nesanci mutanen banza da za su iya sake jefa ka gidan jiya. Koda a shafukan social media media, sai ƙauracewa shafukan banza.

Duk sanda ka zo bacci, ka yi wa kanka hisabin aiyukanka na kullum har tsawon kwana 40. KA RAGE AMFANI DA SOCIAL MEDIA. Son samu, ka nemi journal/diary. Amma sai an haɗa da HAƘURI da NACI, za kuma a ga sauyi a al'amuran ruhi da rayuwa sosai, in sha Allah.

✍️Aliyu M. Ahmad
6th Rabi'ul Awwal, 1445AH
22nd September, 2023CE

#AliyuMAhmad #RayuwaDaNazari #AliMotives 
#MusulunciDaRayuwa #AddiniDaRayuwa

Post a Comment

0 Comments