Ina mamaki mutanen da za su tsinewa wasu mutane, kuma su ci gaba da bibiyar su.
Misali, wasu za su tsine wa 'yan film, Arewa24 ko 'yan TikTok amma kuma suna ci gaba da kallon shirye-shiryensu. Cikin wayarka akwai Labarina da Daɗin Kowa, Kwana Casa'in da Izzar So...
A wasu contents ɗin kuma, sai mutum ya gama kalle ƴan TikTok na rawa, sai ya koma comment ya sa tsinuwa, gobe ma haka... ma'ana yana bibiyarsu akai-akai, ya kalle, ya tsine. Ko tsinewa wasu jaruman 'film', kuma mutum ya ci gaba da kallo film da waɗannan jaruman suka fito.
A cikin hadisin Imran ibn Hussain (2BH - 54AH), ya bayar da labarin wata tafiya da suka tare da Manzon Allah ﷺ, sai wata mata ta tsinewa raƙumarta, a take Manzon Allah ﷺ ya ce ta sauƙe kayan kan raƙumar, ta sake ta, saboda ta tsinewa rakuma, RAƘUMAR TA ZAMA TSINANNA, ba yadda za a yi ka ci gaba da mu'amala da tsinanne abu (Sahih Muslim, 2595).
Ta ya za ka tsinewa 'yan film, ko wasu mutane a social media, kuma ka ci gaba bin tsinannu ba tare da kai ma tsinuwar ta yi tasiri a kanka ko a cikin zuri'arka ba? Ina hankalinmu kam? Akwai abubuwan da suke kasancewa 'ma wa ra'a attabi'a', tasirin tsinuwa yana daga ciki.
#AliyuMAhmad #RayuwaDaNazari
#MusulunciDaRayuwa #AddiniDaRayuwa
0 Comments