Gwal da Lu'u Lu'u

 

 
Ka karanta, za ka fa'idantu:

1. Idan kana son ka riƙa kiyaye zikirin safiya, kar ka tashi daga wajen da ka yi sallar Asuba (a masallaci ne ko a gida) har sai ka yi zikiran, kwata-kwata ba zai wuce 10mins - 15mins ba. Haka ma da maraice, bayan sallar La'asar ko kafin sallar Magrib.

2. Idan kana son kiyaye zikirin bacci, ka riƙa jinkirta sallar Shafa'i da Wuturi zuwa gaf da lokacin da za ka yi bacci, bayan ka idar, sai ka yi addu'o'inka, ka kwanta da alolarka (kar ka yi amfani da waya bayan zikirin, sai in dole ne).

3. Idan kana son tashi sallar dare (tahajjud), ka ɗaura niyya, ka riƙa kwanciya da wuri. Da zarar ka farka tsakar dare ka daure, ka tashi ka yi alola, ka sallaci ko da raka'a 2 ne, sai ka koma ka kwanta.

4. Idan kana son ka riƙa kiyaye sallar jam'i, ka riƙa zama da alola kafin lokacin shiga sallah. Son samu ka riƙa ƙoƙarin zama a msallaci jiran liman, bayan an yi ƙiran sallah, ka yi nafiloli kafin a tayar da sallah.

5. Idan kana ɗaukar lokaci mai tsayi ba ka karanta Alƙur'ani Mai girma, ka nemi malami kana ɗaukar karatu a wajensa (ko da bayan sallar Asuba ko Magriba ne), ai dole ne kana tilawa kafin zuwa ɗaukar karatu. Kana kuma yawaita sauraronsa da wayarka, ko motarka, ka kuma rage jin waƙe-waƙe.

6. Idan sada zumunci yana ma wahala, wataƙila saboda aiyuka, ka riƙa ware yammacin Juma'a (duk sati) kana ziyarta gidajen 'yan uwa, tsakanin La'asar da Magrib. Ko kuma da daddare cikin 'weekends', tsakanin bayan Magrib zuwa bayan sallar Isha'i (duk sati), akwai albarka mai yawa.

7. Idan kana son neman agajin Ubangiji cikin gaggawa kan rufin asiri da yayewar ƙunci, ka dubi wasu cikin makwafta, ko dangi, gidan da yake da mabuƙata, marayu ko zawarawa, ka sayi kayan abinci, ko kayan amfanin yau-da-kullum ka tallafa musu da shi. Idan kana da hali, ka yawaita yanka don neman yardar Allah, kana sadakar da naman, na dabba ne ko tsuntsaye (kaji ko baraye).

8. Idan kana son rufawa kanka asiri daga bashi (loan), ka daina cikin bashi don biyan buƙatun da ba na dole ba. Ka kuma riƙa tattala wani sashe na abin da kake samu a kullum (ko a albashin wata), misali 10% zuwa sama a kullum, a cikin wani asusu na daban (reserved).

9. Idan kana son ka yi mutunci a idon mutane, ka fita sabgar da babu ruwanka, kada shiga sabgar da ba a gayyace ka ba, ka kuma guji (kwaɗayin) abin hannun mutane.

10. Idan kana son cimma wani muradinka, musamman matasa, dole sai ka cire kasala, ka kuma nemi ilimi daga magabata (kwararru). Idan kana son zama kamar wani babba da yake ba ka sha'awa, ka riƙe irin sababin da riƙa kafin ya kai wannan matakin, malami, ko ɗan kasuwa, ko ɗan siyasa, ka kuma yawaita addu'a da neman dacewa a wajen Ubangiji.

✍️Aliyu M. Ahmad
14th Dhul Hijjah, 1444AH
2nd July, 2023CE

#AliyuMAhmad #RayuwaDaNazari #AliMotives

Post a Comment

0 Comments