Tausasa Magana Kan Mata


Matarsa ce ta ɓata masa rai, ya shigo gidansu, yana ta faɗa, yana furta cewa duk mata mahaukata ne, ba su da kirki..., ya kalli fuskar mamansa ya ce, "amma fa umma ban dake".

Ashe babansa yana shigowa, ya ce, "har da uwarka, ka ce ita ma mahaukaciyyar ce, kan me za ka ware taka, ka sa da tawa (saboda kakar tana zaune a gidan), ni uwarka ita ce ke ɓata min rai, ita ce take min hauka".

Duk sanda muka tashi magana kan mata, mu riƙa taunawa, mu riƙa tunawa, iyayenmu mata ne, muna da ƙanne, yayye da 'yan uwa mata.

Muna zuwa asibiti mu ga yadda (wasu) mazaje ke guduwa suna barin matansu? Gidaje nawa ne suke fama da wunya, maigida yana waje zai ci kwai da nama ya bar iyalansa da hamma?

Da yake namiji idan an ɓata masa Shari'a ta ba shi zartarwar saki, ka taɓa zuwa Shariah courts ka saurari yadda wasu mazan ke wulaƙanta mata a gidajen aure sune ke neman haƙƙi?

Ina matan da ba su ji ba, ba su gani ba, suke faɗawa hannu mai auri saki? Namiji ne mai aure kamar yadda canja riga. Ba ki yi laifin komai ba ya maida ki bazawara. Me ya sa kullum idan aka yi saki, an fi ganin laifin mata? Me ya sa idan mata suka kawo ƙarar mazajensu ba a sauraronsu an fi ba su laifi?

A kowanne jinsi, akwai na kirki, akwai na banza. Mu rika tausasa kalmomin kan jinsi mata, iyayenmu, 'yan  uwanmu ne. Musulunci ya ba wa kowa ƴanci da haƙƙi, ya rage namu mu ba wa kowa haƙƙinsa. Wani lokacin, rashin cika haƙƙi ke maida wasu matan 'feminists'. Maza ke zamewa wasu triggers na 'feminism'.

Allah ya haɗa mu da abokan zama nagari 🙏

✍Aliyu M. Ahmad
4th Safar, 1445AH
21st August, 2023CE

#AliyuMAhmad #RayuwaDaNazari
#TausasaMagaKanMata #MusulunciDaRayuwa

Post a Comment

0 Comments