YAYA DA ƘANI


Wasu waki'o'i 2 na ɗauko a cikin 'memoir' masu cike da darussa:

• NA FARKO:

Yaya da ƙani ne, 'yan gida ɗaya, uwa-daya, uba-ɗaya. Yayan yana da sha'awar karatun boko sosai, shi kuwa ƙanin, yaron 'yan siyasa ne, ya fi gane buga-buga.

Kullum yayan yana goranta masa, ya ƙi karatu, sai sharholiya. A 2016, yayan ya kammala makaranta ya dawo shi ma yana buga-buga samun abin rufin asiri.

Cikin ikon Allah, wannan ƙanin dake bin 'yan siyasa, 2018/2019 da ubangidansa ya ke rabon offer, sai wannan ƙanin ya ce da Ubangidansa, ka san na yi bauta a gidanka, kuma na ga kana raba aiki ban da ni.

Ubangidan ya ce, to ana raba aiki ne ga masu takardar karatu, kai kuma ba ka yi ba. Ya ce, indai na kai ka min, to ka ban aikin ina da ɗan uwa da ya yi karatu, idan aka masa kamar ni ka yi wa.

Wanda bai yi karatun bokon nan ba, shi ne ya yi wa mai boko sanadin samun aiki a Abuja.

• NA BIYU:

Su ma waɗannan 'yan gida ɗaya ne, sun kammala diploma 2017. Ɗayan ya fita da "Distinction" (kamar First Class kenan), 'yan uwansa sai suka yi ta ɗora shi a status da Facebook kan ya yi kwazo. 

Ɗayan kuma ya fita da 'Upper', ba don ba shi da ƙoƙari ba, sai don rashin maida hankali. Shi bai samu kulawa irin ta wancan ɗan uwan ba. Ya damu, nake ce masa, ka yi addu'ar Allah ya sanyawa sakamako albarka kawai.

A 2018, mai Upper ya samu aiki da Judiciary, yanzu haka yana 'in-service'. Ga scholarship, ya tafi ƙarin karatu, ga aiki, permanent and pensionable. A lokacin da ya samu 'offer', ya ce, an yi masa 'status' kamar yadda aka yi wa ɗan uwansa mai 'distinction'. 

✍️Aliyu M. Ahmad
26th Sha'aban, 1444AH
16th March, 2023CE

#AliyuMAhmad #RayuwaDaNazari #AliyusMemoir 

Photo credit: Clipart Library

Post a Comment

0 Comments