A kullum ina faɗawa kaina, idan akwai wani da zai ƙulla min sharri, ba wanda ya wuce NI kaina. Idan kuma akwai mutumin da zai so ni da alheri, ba wanda ya wuce NI kaina.
Idan wata ni'ima ce Allah ya min, har wani yake son yi min sharri ko hassada, gangancina ne na rashin neman tsari a wajen Allah zai sa a yi galaba a kaina. Idan ba na zikiri/wurudi safiya da maraice, ko a lokacin bacci, a kowanne motsi, ta ya duk wani sharri da za a jefo ba zai same ni ba?
Idan kullum ba ni da aiki sai kasala, sai son hutu da bacci, ba na fita na nema kamar sauran abokaina, ni ba neman ilimi ba, kuma ina da hali; ta ya zan tsammani wani daga sama ya zo ya taimake ni bayan na kasa taimakon kaina? Idan ma akwai mai taimako, ai sai idan ya ga zan iya ne, sai ya kama hannuna ya cicciɓa ni, amma ina fankan-fiyau, ba na iya tsinana komai, babu mai kula ni, gaskiya kenan!
Ubangiji ya haramta haram, ya halas halal. Na san daidai da akasinsa. Idan na bi son zuciyata dole na girbe abin da na shuka na sharri ko alheri, a nan duniya ko a ƙiyama. Ni zan kare ƙimar kaina, na mutunta kaina, tukun a mutunta ni.
Shi ya sa a duk lokacin Manzon Allah ﷺ zai yi 'khutbatul haja', sai ya nemi tsarin Allah ga sharrin kai: "ونعوذ بالله من شرإن الحمد لله نستعينه ونستغفره ونعوذ بالله من شرور أنفسنا وسيئات أعمالنا... " Ma'ana: "...kuma muna neman tsarin Allah daga sharrin kawunanmu da munanan aiyukanmu..." (Abu Dawud, 2118).
Idan na tashi na motsa, Allah zai taimake ni. Idan na kiyaye dokokin Allah (ba na saɓo ba na neman kowa da sharri), na kuma nemi tsarinsa, haƙiƙa zai tsare ni. Idan kuwa na yi kasala, sai Ubangiji ya bar ni da halina. Na san abin da zan iya, na san abin da ya fi ƙarfina. Ba mai bi na da sharri kamar kaina, babu mai bi na da alheri kamar kaina, zaɓi ya rage gare ni.
"ما أصابك من حسنة فمن الله وما أصابك من سيئة فمن نفسك..."
An-Nisa'i, aya ta 79
✍️Aliyu M. Ahmad
28th Sha'aban, 1444AH
21st March, 2023CE
#AliyuMAhmad #RayuwaDaNazari
0 Comments