Officer



Yadda duniya yau ta koma digital, ake komai cikin sauri, haka rayuwar yau take saurin karantar da darusa ga masu hankali da nazari.

A 2014, watarana na zo weekend daga JSCILS (lokacin ina diploma in Law), da safiya Litinin zan je tashe na koma makaranta sai na haɗu da wani abokina da a lokacin yana zana WAEC. Na gan shi cikin uniform yana sauri, sai na ce: 

"Kai wai har yanzu ba ka gama 'secondary' ba?" Ya ce, Wallahi! Da ɗan saura, ai lokaci ne." Da alama dai a fuskarsa bai ji daɗin tambayar ba.

A cikin December, 2022; lokacin mun dawo hutun mid-semester, Xmas da New Year, sai muka haɗu da shi, yake ce min, "aurena fa ƙarshen January, 2023: Allah ya sa kana gari".

Na ce masa, gaskiya lokacin muna 'final exams', sai dai na yi maka fatan alheri. Sai ya ce "kai wai har yanzu ba ka gama digirin ba?" Sai waccar maganar ta 2014 (shekaru 8 baya) ta faɗo min.

Abokina bayan ya gama secondary 2014, ba jira ya sami admission 2015; ya kammala digiri a 2020 daf da fara COVID-19. Yana cikin NYSC ya cike "immigration," bai yi wata 2 ba da kammala service ba ya sami "immigration" 2021. A August, 2021 aka musu POP su 430.

Na kammala secondary 2012, diploma 2015, digiri 2022/2023, ban karɓi statement of result ba, balle NYSC. Officer ya kammala secondary 2014, ya kammala digiri 2020, ya sami aiki 2021, ya yi aure 2023. Don yau ka wuce wani da taku ɗaya yau, gobe zai iya wuce ka da taku 100 ko 1000, ba ruwan Allah. "Kyakkyawar kalma ma sadaka".

✍️Aliyu M. Ahmad
23rd Sha'aban, 1444AH
15th March, 2023CE

#AliyuMAhmad #RayuwaDaNazari #AliyusMemoir 

Photo credit: Ogundiran Dolapo

Post a Comment

0 Comments