Mu faɗawa kanmu wata gaskiya man!
Matuƙar muna amfani da 'social media', za mu riƙa cin karo da 'video contents' na comedy. Misali a Nijeriya, akwai na Kudu da Arewa, kuma ko muna so, ko ba ma so, za a yi, za kuma mu kalla, 'ya'yanmu za su kalla, saboda 'algorithm' na 'Facebook Reels' da 'Tiktok' kan iya kawo har abin da ba ka 'following' na kirki da na banza.
Abin da zai baka haushi, yawancin masu 'skits' namu na Hausawa, bat*a tafi yawa, ba wata fasaha ƙirƙira ta nuna zamantakewar Bahaushe, ko ci gaban ɗan Adam, sai ɗaiɗaiku. Amma na Kudu, da yawa suna 'filming' da yake isar da wani saƙo, koda sun haɗa da mata ko bat*an. Misalansu da yawa; Brain Jotter, Sabinus, Frank Donga, Mark Angels, Sydney, Favour Oma, OGB Recent, Sirbalo, Twizzy, Josh4Funny.. kai da Freaky-Freaky Mr. Macaroni, ai duka muna ganin contents ɗinsu.
21st idan mutanenmu suka yi yi burus, ba ruwansu da harkar hada 'skits', ko film na tarbiyya, kuma akwai masu basirar iya ƙirƙira, da rubuce-rubuce, waɗancan mutanen banza za su yi yaɗa sharholiya, kuma kuɗi ake samu daga yawan engagements, makudai! Ba wani abu da Hausawa za su nunawa duniya da adabi a media sai sharholiya? Ina al'adarmu, addininmu da tsarin zamantakewarmu?
A 'content creators' na Arewa, idan ka cire irinsu Hausa Guy, sai wasu ɗaiɗaiku; sai dai ka ga wata maroƙiyya, tana bin maza masu mota, ka rasa wane saƙo take son isarwa... kuma suna samun engagements 100k, 500k, 1m+ su waye ke 'following' da yi musu 'impression'? Social media ta wuce yadda muke kallonta, rayuwa ce, makaranta ce, duniya ce guda...
Al'umma ba za ta rayuwa ba adabi ba, gaskiyar magana kenan, musamman don neman nishaɗi. A da, ana ƙirƙirar tatsuniya, a kuma isar da sakon tarbiyyar cikinta, yanzu 'skits' ake a 'social media'. Da Shari'a ta haramta shan giya, sai ta ce, "كلو من طيبات ما رزقناكم" (Bakara aya ta 72). Lokacin da 'yan aike suka je wa Annabi Lut عليه السلام, mutanen gari suka so afka musu, cewa ya yi "يا قوم هؤلاء بناتي هن أطهر لكم" (Hud, aya ta 78)... wannan shi ne tafiya da zamani, duk abin da yake na rashin ɗa'a, akwai 'alternative' ɗinsa na ɗa'a.
Faɗakarwa ce!
✍️Aliyu M. Ahmad
2nd Sha'aban, 1444AH
23rd Febuary, 2023CE
#AliyuMAhmad
#RayuwaDaNazari
#RealityTalk
Malumfashi Ibrahim, Hasheem Abdallah, Muhammad Mahmud, Ibrahiym A. El-Caleel, Sunusi Umar Sadiq, Adam Sharada, Sulaiman Badamasi, Aliyu Aliyu, A.I. Sabo, Salim Yunusa, Badamasi Aliyu Abdullahi, Faruk Kafin Hausa, Amir Muhammad Harbo...
0 Comments