Public Comments Display


Masu yi wa 'yan uwa mata 'comment' a FACEBOOK STORIES, sai ana kiyayewa da mutunci, yanzu FACEBOOK sun gyara, ana iya karanta 'COMMENT(S)' ɗin 'story' kamar yadda ake iya karanta 'comment(s) a 'public posting(s)'.

A kula! Kafin ka rubuta 'comment', ka duba a 'text box' za ka ga an rubuta:


👉 'write a comment'
Kowa cikin 'friend(s)' da 'viewer(s)' zai ga abin da rubutu, ko kuma


👉 'write a message'

Wannan kuma iya mai 'story' ne kaɗai zai ga, ta cikin 'Messenger'.

A kiyaye! A san ire-iren 'comment(s)' da za a ana rubutawa/turawa ƙannenmu, yayyenmu da iyayenmu mata, domin yanzu muna iya gani, girma da mutunci kuma yana (iya) faɗuwa. Babban mutum, mai mutunci yana cewa ƙaramar yarinya, 'yane?', ko 'kin yi kyau?', 'ba ni lambar wayarki!', 'ina sonki', 'hi!'... don Allah a daina!

Idan kina son ki saita yadda duk wanda ya miki 'comment' a kan 'story' ya zama 'public', kafin ki 'publishing story', shiga 'Story Privacy' > 'Comments', sai ki 'switching', daga nan duk wanda ya miki magana (comment) a kan story, 'friends' da 'story viewers' za su ga me ya rubuta.




#AliyuMAhmad #RayuwaDaNazari #Facebook #FasaharZamani

Post a Comment

0 Comments