#AliyuAndTheLaw: Mu fahimci wani abu game da tsarin cin zaɓen shugaban ƙasa, kamar yadda sashe na 134 na Constitution (CFRN, 2011 amend.) ya ambata:
Mutum ba zai ci zaben shugaban ƙasa ba, har sai ya samu 25%+ na yawan ƙuri'u daga 2/3 na jihohin Nigeria ciki har da Abuja kamar yadda sashe na 134(1)(a) na CFRN ya ambata.
Abin da ake nufi anan shi ne, Nijeriya tana da jihohi 36, 2/3 na yawan jihohin Nijeriya shi ne jihohi 24. To, a ƙalla sai ɗan takara ya samun abin da bai gaza 25% daga cikin yawan ƙuri'a da a kaɗa a kowacce jiha ba, daga jihohi 24 ko fiye, koda kuwa ya fi kowa yawan ƙuri'a (s. 134(3)(b) CFRN).
* Misalin 25% na yawan ƙuri'un jiha 'A' mai ƙuri'u 3,678,920; shi ne 919,730 zuwa sama.
* Misalin 25% na yawan ƙuri'un jiha 'B' mai ƙuri'u 1,000,000; shi ne 250,000 zuwa sama.
Misali, idan party AX ta ci ƙuri'a 12,593,678 kuma, ta samu 25% daga jihohi 20 cikin 36 har da FCT. Shi kuma party AY ya ci ƙuri'u 11,083,768, ya kuma samu 25% na kuri'un jihohi 26. A ƙa'ida, party AY mai ƙuri'a miliyan 11 shi ne ya ci zaɓe da yawan jihohi, ba jam'iyyar AX ba mai ƙuri'u miliyan 12 ba.
Idan kuma kowanne ɗan takara daga party AY da AX sun kawo jihohi 24 ko fiye da 25%, sai a duba wanda yafi yawan kuri'a, shi ne ya ci zaɓe.
Idan kuma duk cikin 'yan takara sun gaza kawo ƙa'idar sashe na 134(2), na 25% daga jihohi 24, INEC za ta sake shirya zaɓe a zagaye na biyu tsakanin 'yan takara 2 da suka fi yawan kuri'u sati ɗaya bayan zaɓe (s. 134(4) & (5) CFRN).
✍️Aliyu M. Ahmad
5th Sha'aban, 1444AH
26th February, 2023CE
#AliyuMAhmad #RayuwaDaNazari
#NigeriaDecides #Siyasa
0 Comments