Matsalarmu!


#RealityTalk:

Za mu iya tattauna matsaloli 10, amma ba za mu iya zama mu magance koda 1 ba, shi kansa irin wannan salon matsala ne.

Idan alal misali cikin unguwa mai gidaje 50 ana rashin ruwa, ma'anar ana buƙatar famfon ruwa, 'submersible' ko 'borehole'. Aikin somo (submersible) 7 ph zai iya cin ₦400k. Duk cikin unguwar da ake kuka rashin ruwa da gyara ko siyan kayan aikinsa ya kai ₦400k, ka san aikin ya fi ƙarfi mutum 1 kaɗai.

Ka yi lissafi, gidaje 50, idan kowanne gida zai na bayar da 'contribution' na ₦1k a duk sati, cikin wata 2 za a magance matsalar da za a tsaya jiran shekara da shekarun jiran wani ya zo ya magance. Ko zagin waɗanɗa ake yi wa kallon suna da arzƙin cikin unguwa sun kasa siyawa unguwa famfo. A #reality, jarinsa zai karya ya yi muku famfo? Ko kuwa ta gidansa da danginsa zai ji? Shi da ba ɗan siyasa ba.

Lissafa, ₦1 x 50 x 8 = ₦400,000.

Idan matsalar ₦400k ta taso, ni kaɗai wataƙila ba ni da ₦400k, amma idan aka haɗa ƙarfi-da-ƙarfe, za a iya magance matsalar da ba ni kaɗai ta shafa ba. Maimakon mu zauna muna maganganu kan matsalarmu, sai mu zauna shekara da shekaru muna zagin wani ɗan majalissa, ko chairman, ko wani mai arziƙin da ba mu san halin da yake ciki ba.

Idan matsalar karatu ce, yaranmu suna makarantu gwamnati, ba sa iya Turanci da Larabci, akwai 'graduates' ko masu ND da NCE, su yi kungiya suna koyar da ƙannensu koda 1hr ne a kwana 3 ko 2 cikin sati. Matsalarmu, mukan ɗauka certificate shi ne ilimi.

Idan kuma a cikin gida ne, akwai samari 3 zuwa 5 da ƙannensu sun kasa zuwa makaranta saboda ba kuɗi. Wataƙila idan mutum 1 ne, ba zai iya ɗaukar nauyinsu ba, amma idan samari 5 na gida suka haɗa ƙarfi-da-ƙarfe, sai su cicciɓa ƙannensu, maimakon kowa ya kauda kai. Duk yaron da ya san an masa, idan ya samu dama shi ma zai yi wa wasu.

Idan matsalar sana'a ce, akwai matasa masu sana'o'in ɗinki, kanikanci, kasuwanci... manyan unguwa sai su zauna su rarraba yara masu tasowa ga wasu domin su koya musu sana'o'i.

Mun iya zama mu yi gulmar wane ya kasa riƙe 'ya'yansa, ko 'ya'yan wane sun lalace, amma ba za mu iya huɓɓasa ba wajen taimakon rayuwarsu. Kowa ya maida 'ya'yansa su kaɗai ne nasa. Idan yaro ya zama ɓarawo, kowa na ɗarɗar da dukiyarsa. Ba wanda zai iya sa wayarsa caji a cikin masallacin unguwa sai yana tunanin a cikin yaran unguwa wani zai zo ya sace. Ba a iya ajiye babur a ƙofar gida. Yara sun taso ba gata, ba mai kula da su, sun taso suna rarrafa rayuwarsu su kaiɗai, kuna tunani ko tsammanin idan sun samu dama za su waiwaye ku?

✍️Aliyu M. Ahmad 
6th Sha'aban, 1444AH
27th February, 2023CE

#AliyuMAhmad #RayuwaDaNazari #LetsMakeBetter

Post a Comment

0 Comments