محفظ الوحيين El-Mohafez




Ita ma manhajar Alƙur'ani Mai girma ce mai ɗauke massahif na ruwayoyin Alƙur'ani 20 (Hafs, Warsh, Ƙalon, Adduwry, Assusi, Khilaf, Ƙunbil...) Tafsirai 5; Masir, Maudu'iy, Jaza'iry, Ibn Kathir da Mukhtasar.

A littafan hadisai akwai Bukhari, Muslim, Umdatul Ahkam da Arba'unan Nawawi. A mutun na sauran littafai kuma, akwai Al-Jazariyya, Al-Salsabil Al-Shafi', Alƙawa'idul Fikhiyya, Tufhatul Atfal, Shatibiyya, Albaiƙuniyya, Arrahbiyya, Fathul Karim fi Tahrir, Almufid fi Ilmil Tajwid, Nuniyyat, Azw Al-Turuƙ, Hidayatul Murtab, da sauransu.

Wani abin sha'awa da wannan 'app', da Alƙur'ani, littafan hadisai da sauran 'mutun' duk ana jin 'audio' nasu daga kan 'app' ɗin. Ana kuma iya searching na wata kalma, ko jumla a cikinsu. Za ka iya amfani da 'app' ɗin, da Turanci ko Larabci.

Idan ma kana son tsara 'khatma' (sauƙe Alkur'ani) cikin wasu kwanaki, za ka iya 'scheduling' cikin app ɗin, daga wurin da za ka fara, izu nawa za ka na yi a kullum, a wasu ranaku, wane lokaci zuwa wane lokaci, akwai kuma 'alarm' na tunatarwa; za kuma ka iya 'bookmark' ko sanya alama na wurin da ka tsaya. Akwai 'app guide' da zai ganar da kai yadda za ka yi amfani da 'El-Mohafez' sosai.

Allah ya amfana.

Akwai 'app' ɗin a Playstore (Android) da Appstore (iPhone), ga link 👉 www.elmohafez.com

Allah ya amfana.

✍️Aliyu M. Ahmad
19th Sha'aban, 1444AH
11th March, 2023

#AliyuMAhmad #RayuwaDaNazari #FasaharZamani #GuzurinRamadhan

Post a Comment

0 Comments