Kafin Ka Yi Bacci


Duk wanda ya kwanta bacci a yau:
✓ Bai kwanta da haushin kowa ba,
✓ Bai ƙullaci kowa ba,
✓ Bai ci haƙƙin kowa ba;
Idan Ubangiji ya ƙaddara aka ɗauki ransa a wannan daren, insha Allahu ba abin zai hana shi shiga Aljanna.

Duk wanda kafin ya kwanta bacci:
✓ Ya yi alola,
✓ Ya karanta Ayatul Kursiyu, Amanar Rasul da Suratul Mulk, ya kuma shafe jikinsa da Ikhlas, Falaki da Nasi (x3).
✓ Ya karanta sauran zikirai na bacci;
Insha'Allahu za a kare shi daga sharrin dukkan abin hallitta har zuwa wayewar gari.

Duk wanda kafin ya kwanta bacci:
✓ Ya sami sallar Isha'i (da ta Asuba) a cikin jam'i, za a rubutu masa kamar ya sallaci dare (baki ɗaya).

#AliyuMAhmad
#RayuwaDaNazari

Post a Comment

0 Comments