Tsakanin Gaskiya Da Adalci


Ko wannan ne ya sa ake ce wa "SHARIA SAƁANIN HANKALI CE?" Amma a haƙiƙar gaskiya, da dalilan ilimin Shari'a, Shari'a ba ta saɓawa da hankali.

Kotu ba ta zalunci! "Kotu waje ne na yi wa kowa adalci, ko da kotu ta tabbatar ma da laifi ta hukunta ka, wannan shi ne adalcin kotu a kanka." Barr. Dalhat Jibril Turaki 

----------------------------------

Misali, Mallam Sukairaj Hafiz Imam ya ce:

"Idan ka ba wa abokinka bashin ₦50,000 ba tare da shedu ba. Bayan wani lokaci ka ce, wane ina son ka dawo mini da kuɗina domin ina da buƙatu.

Shi kuma sai ya ce, ba ka bi na ko sisi!

In ka garzaya zuwa kotu, abu na farko da Alƙali zai fara tambayarka shi ne, kana da shedu? A lokacin da bakinka za ka ce, A'a!

Alƙali zai nemi abokinka ya yi rantsuwa. Babu kunya babu tsoron Allah ya yi rantsuwa a kan ba ka bin sa ko sisi.

* 𝑾𝒂𝒏𝒏𝒂𝒏 𝒔𝒉𝒊 𝒏𝒆 𝒘𝒂𝒏𝒏𝒂𝒏 ƙ𝒂'𝒊𝒅𝒂𝒓 𝒕𝒂 𝑴𝒂𝒏𝒛𝒐𝒏 𝑨𝒍𝒍𝒂𝒉 ﷺ 𝒌𝒆 𝒄𝒆𝒘𝒂: "البينة على المدعي واليمين على من انكر" (𝑩𝒖𝒌𝒉𝒂𝒓𝒊, 4552).

Alƙali zai ce tabbas haka maganar take, ba ka bin sa ko sisi tun da ya rantse. Wannan shi ake ƙira ADALCI.

Amma haƙiƙanin zance kana bin abokinka ₦50,000  wannan ita ake ƙira 'GASKIYA''

Idan haka ne, ko da dalili ko babu dalili ita gaskiya ɗaya ce ba ta canzawa. Amma Adalci yana canzawa da canzawar shedu da dalilai.

Duk in da gaskiya take akwai adalci a wurin amma ba duk in da adalci yake ba ne gaskiya take.

Gaskiya Allah ne kaɗai ya san ta sai wasu tsirarin mutane, amma adalci yana da fuskoki da dama, zai iya canzawa daga hagu zuwa dama a cikin mas'ala ɗaya."

----------------------------------

TAMBIHI

1. Shari'a tana amfani da abin da yake 'fact', ya bayyana zahiri a gabanta, a 'juducial process' za a tabbatar, ko a rushe.

2. Ko don kare mutuncinka gobe, ka roƙi Ubangiji ya ba ka rufin asirin samun a tsaye ma a wajen Shari'a. Hujjarka (da ta bayyana), ita ce jarin nasararka a gaban kotu, ba gaskiyarka ko akasinta ta ɓoye ba.

3. Tabbatar da shaida ko shedu, ko rushe shaidar shedu, aikin lauyoyi ne, su yi 'examination', 're-examination' da 'cross-examination'; (su kuma tsakaninsu da Ubangijinsu ne). Alkali aikinsa, ya yi amfani da abin da aka gabatar masa, ya yi hukunci.

#AliyuMAhmad #RayuwaDaNazari #AliyuAndTheLaw

Post a Comment

0 Comments