Ci gaban 👉 bit.ly/3SV0ExG
Ina Æ™ara maimaitawa! Domin mu ji daÉ—in rayuwarmu, ba iya kula da zahiri (ie. cin abinci mai kyau, muhalli, sutura...) ne kaÉ—ai ba ne, a’a; wajibinmu ne, mu riÆ™a kula da tunaninmu da abubuwan da muke ji a cikin zukatanmu (emotional feelings).
‘Emotional intelligence’ kuma, shi ne, sanin yadda za ka sarrafa kanka kan komai, ka kuma fahimci abin da ke kewaye da kai, da yadda za ka yi mu’amala da su cikin ruwan sanyi, ba tare da cutar da kanka ko waninka (abokin mu’amala) ba.
Paranoia: ‘personality disorder’ ce da ke sanya wa mutum 'tsoro', 'zargi', ko 'Æ™in yarda/amici', wacce take yanke wa ‘matasa’ musamman masu soyayya, shirin aure, da ma (wasu) masu aure kwanciyar hankali game da rayuwarsu da ‘mace’, ko mace kan namiji.
Mu fahimta, akwai bambanci tsakanin ‘tsoro, zargi da Æ™in yarda’ (paranoia) da kuma ‘kishi’ (jealousy). Mutumin mai ‘paranoia’ zai cutar da abokin alaÆ™arsa (budurwa ko mace, ko saurayi ko miji), ya kuma cutar da kansa (a tunani).
Irin waÉ—annan, sune masu kafawa mace sharuÉ—É—an alaÆ™a da wasu mazajen, ciki har da ‘yan uwanta na jini maza (cousins, uncles…) ko tsofin samari da samari, saboda tsoron kada ta yaudare su, ko su kwace masa ita. Ana samun wanda, hatta mace, idan za ta fita daga gidansu, sai ya ba ta izini. Wani har makaranta ‘Islamiyya’, ko 'wajen É—aukar karatu'; zai ya hana ta zuwa, idan ya ji wani malami ya ce yana sonta.
Idan kwa zai Æ™ira ta a waya, ya ji ‘on waiting’, sai ya hau bincike. Akai-akai, yana duba wayarta, da nufin lamumo mutanen da suke mu’amala da ita… a dole dai, SHI KAÆŠAI ZA TA KULA. Yana cutar da kansa (da Æ™uncin tunani), da kuma ita (a takure). WANI MA BA SHIRIN AURE NE DA SHI BA, zallar soyayyar ce kurum, ya hana ta kula masu sonta aure, wannan ma kuma zalunci ne.
Ana samun irin wannnan matsalar a yayin mutum ya ji labarin rayuwar wasu, ko abin da ake yawan faÉ—a game soyayya. Ita kuma soyayya, abu biyu ne muhimman, YARDA (aminci) da RIƘON AMANA. Mace a É—abi’arta za ta iya kula mazaje da dama, amma zuciyarta ta namiji É—aya ce; idan ka tabbatar kai ne É—ayan, shikenan! Mace, ce wa za a yi, ana sonta, ba wai ita ce, za ta ce, tana so ba (mu gane bambancin).
Idan kana alaƙa da mace, akwai matakan alaƙar da ita, da haƙƙoƙi da ya kamata ka sani, ka kiyaye, don kar ka riƙa cutar da kanka a tunani, da kuma ita kanta, ka takura mata:
• Na farko, idan neman soyayyarta ka ke, BA A CE KAR KA YI KISHI BA, amma, matuÆ™ar iyaye ba su yi yarjejjeniyar nema ma aurenta ba, ba ka da ikon hana ta kula wani mai sonta, domin babu ‘khitba’ tsakaninku.
Kar ka ce sai ka san duk wani motsinta. Mace tana da ikon yin uzuri na karan kai, ta je wuraren da take da uzuri, ta yi mu’amala da ‘yan uwanta na zumunci, da abokanta na makaranta, matuÆ™ar ba alfasha za ta yi ba. Wannan zurfafawar, hurumin iyayenta ne!
• Na biyu, bayan iyayenka sun shigar da magana, an yi ‘khitba’, an amince za a ba ka aurenta, kana da ikon hana ta kula wasu, saboda Manzon Allah ï·º cikin hadisi, ya haramta nema kan nema [Bukhari, 5142].
Ko ita idan ta ba wa wani damar soyayya, a wannan matakin, bayan ‘khitba’, TA YI ZALUNCI “a little attention, can go a long way.” Wannan ke sa wasu matan, bayan sun yi aure, suke karya ‘SIM card’ É—insu, don yanke alaÆ™arsu da samarin da ba su sami aurenta ba.
Wata alaÆ™ar kuma, koda mace ta so yanke ta bayan ta yi aure, wancan (ex) zai iya ja ma ta matsala, saboda saÉ“a waccar Æ™a’idar, mai alaÆ™a ta “SRPD”, a lokacin da aka sami “psychological dislocations”, sai ka ga aure ya lalace.
• Na uku, bayan aure, matsalar “paranoia” ce ke hana wani mijin matarsa yin aiki, saboda tsoron kar ta ci amanarsa a fitarta wajen aiki, koda matar tana taimaka musu da aikinta a rayuwarsu ta cikin gida,. Wannan na ginuwa saboda yawan jin labarin “infidelity” (cin amana) na matan aure ke yi, musamman tare da tsofin samarinsu, koda alaÆ™ar “platonic” ce (ba ta kai su ga sanin juna ba).
A cikin AlÆ™ur’ani, Suratul An-Nasa’i; aya ta 34: a Shari’a, mace tana Æ™arÆ™ashin kulawar namiji, tun daga tasowarta, aurenta, da tsufanta, saboda hikimomi da ke lulluÉ“e cikin haka. Haka kuma yake a al’adun al’umomin duniya, ko ba addini.
Kishin mace a kowanne mataki abu ne mai kyau, amma ka iya bambance tsakanin kishi (jealousy) da zafin kishi ma sa zargi, Æ™in yarda (paranoia); akwai bambanci tsakanin 'kulawa' da kuma 'takurawa'. Ka bar abun da Allah Ya lulluÉ“e, ka yi mu'amala da zahiri. Mai matsalar ‘paranoia’ yana buÆ™atar ganin likitan kwakwalwa, saboda ‘disorder’ ce.
✍️ Aliyu M. Ahmad
9th Rabi’ul Awwal, 1444AH
5th October, 2022CE
#AliyuMAhmad
#RayuwaDaNazari
0 Comments