Ba A Iyawa Mutum

AURE 
Ba ka yi ba, ana ma gori;
Ana cewa, ka ƙi aure, yaushe za ka yi aure?

BAYAN KA YI AURE
Ana ma gorin zama da mace ɗaya;
Yaushe za ka ƙara aure?

Idan ka yi ta biyun ma, za a tambaye ka;
Yaushe za ka cike ta uku? 
Yaushe za ka rufe ƙofa?

HAIHUWA
Bayan 'yan watanni da tarewar amaryar, 
Yaushe za mu zo suna?
Har yanzu mun ji shiru.

Bayan yaye ɗan fari (first born), 
Yaushe za a yi wa 'Faruk' ƙani?
Yaushe za a yi wa 'Siddiƙa' ƙanwa?

Don abokanka sun yi aure, 
Kai ba ka ka yi ba, normal ne ✅

Ƙannenka sun yi aure, 
Har yanzu ba ka yi ba, normal ne ✅

Don ka/kin yi aure, wani/wata bai/ba ta yi ba, normal ne ✅ Wani na can a asibiti a kwance, ba a ce dole sai ka yi jinya ba. Yanzu haka ana ɗaukar ran wani, ba a ce sai ka mutu ba kai ba. Abu ne na lokaci, da dama.

Ana aure ne lokacin da aka shirya yinsa, da shirin ɗaukar nauyin iyali har tsawon rayuwarka, ba wanda zai tambaye ka ko kana da wannan tanadin, ko kuma zai taimaka ma ta wannan ɓangaren.

Maimakon mutane su damu da rayuwarsu, me ya sa damuwa da rayuwar wasu; sun ƙi aure, musamman ga 'ya'ya mata. Kwaciyar hankali, nutsuwa da samun rufin asiri abubuwan lura ne.

Kai! Idan da ranka ma, wataran sai wani ya ce ma, WAI HAR YANZU BA KA MUTU BA?

✍️ Aliyu M. Ahmad
6th Rabi'ul Awwal, 1444AH
1st October, 2022CE

#AliyuMAhmad
#RayuwaDaNazari

Post a Comment

0 Comments