Computer


"Ina da COMPUTER sama da shekara, amma in ban da kallon 'films' ba abin da na iya da ita, sai dai na buɗe, na rufe" - haka wasu ke faɗa.

Amfanin 'computer' na da yawa, ciki har da kallon 'videos', da sauraran sauti (audios). Amma idan ka taƙaita ga iya kallo a kullum, 'computer' a wajenta, ba ta da bambanci da 'DVD Player'.

DVD Player amfaninta kallo ne, a sa DVD/CD disk, ko 'memory card', ko 'flash drive', a kalli films; ko a kunna wani sauti (audio); iya abin da kai ma kake yi da taka 'computer' kenan.

Idan kana da computer, a matsayin "end-user", a ƙalla ka yi ƙoƙarin iya 'basics' abubuwan da ake amfani na yau da kullum:

1. Microsoft Office Suite/Packages
• Microsoft Word (typing da tabulation), 
• Microsoft Power Point (slides) 
• Microsoft Excel (spreadsheet da lissafi)...
ko iya waɗannan ma, ka ƙoƙarin ka iya.

2. Internet(work)
• E-mailing (turawa ko aika saƙo ta 'e-mail')
• Search engine (browsing a 'Google', da sauransu)
• Social networking a computer (ka iya shiga Facebook, Twitter... ta computer)

3. Files Operations
Ka iya sanin yadda za ka canjawa files wuri, ko suna, ko gogewa, ko kwafa, ko adanawa, ko turawa zuwa wasu devices ɗin, ko priting document, da sauransu.

4. Sarrafa Cikin Computer
• Ka iya sa wa 'computer security password', da canja shi.
• Sa 'computer' a lock, ko 'hibernation'
• Ka iya ragewa ko ƙarawa screen ɗin computer haske, 
• Ka iya ɗora sabon application (installation), ko cirewa (uninstallation), ko updating (idan da buƙata).

Mu sani, tara Anti-Virus a computer, ba abin da yake jawowa, sai ma ƙara virus(es). Da yawa cikin wasu '(free) anti-viruses', suma virus ɗin ne. Idan kana amfani Windows (kusan da shi aka fi amfani), idan dai ba za ka sayi 'Anti-Virus' na kuɗi ba, akwai "Windows Defender" ko "Microsoft Essential Security", ka riƙa updating na sa a akai-akai (koda bayan sati-sati ne), zai wadatar ma.

Ba abin damuwa ba ne, don ba ka da 'computer'; wayar hannunka ma (Android ko iPhone), ko 'tablet' su ma 'computers' ne. Operations ɗaiɗaiku ne wayar hannu ba ta yi. Za ka iya typing da WPS, browsing a Google, ko tura saƙon 'email', graphic design, editing na videos ko audio, publishing a webpages...

Ba a gaggawa a koyo, ana koya a hankali, ɗaya-bayan-ɗaya; da sa naci, haƙuri da juriya, da kuma gwaji (practical) akai-akai. Akwai tutorials da yawa a  Youtube, na yadda za ka iya sarrafa "computer" don ƙara samun kwarewa.

✍️Aliyu M. Ahmad
9th Rabi'ul Awwal, 1444AH
5th October, 2022CE

#AliyuMAhmad #FasaharZamani 
#TheNorth #RayuwaDaNazari

Post a Comment

0 Comments