“Facebook dandali ne da ya ba wa mutanen da suka san junansu (abokan makaranta ko na wajen aiki) damar sake ƙulla alaƙa (domin tabbatar da zumunci), da kuma ƙulla sabuwar alaƙa da wasu sabbin mutane (mabanbanta daga sassan duniya daban-daban). Cin amana a Facebook kuma, abu ne da ya zama ruwan dare (saboda kamar kowacce kafa, shi ma Facebook haɗe yake da mutanen ƙwarai da na banza).
Wata abotar a Facebook, (tsakanin namiji da mace) takan iya kai su har ga aure, wata kuma kan iya haddasa fitina da rashin yarda tsakanin ɓangarorin biyu, har ta kai ga rabuwar auren da ya jima (ga wasu), ko saki, a lokacin da ɗaya daga cikin ma’aurata (ko abokin mu'amala) ya gano cewa, ana cin amanarsa a Facebook. Saboda wata mummunar alaƙar a Facebook, takan iya jawo ga cin amana ta zahiri (wa’iyyazubillah).
Cin amana a Facebook kan iya zuwa ta fuskoki da dama; wata har takan kai ga alfasha, ko ƙulla soyayya, ko dukkan biyun. Alfasha kuma a ‘social media’ ta haɗa har da musayar hotuna ko bidiyon juna (visual contents), ko ta sauti (voice note), ko a rubuce (chats) da kan iya tada hankalin juna, ga masu aure ko marasa aure ne (da wasu mutanen da suka sani ko waɗanda ba su ma sansu ba). Cin amana a Facebook shi ne, mutum ya nemi jin daɗi a Facebook daga wanda babu alaƙar aure (ko sanayya) a tsakaninsu.
Wani ya taɓa wallafa cewa: yana tare da matarsa kusan shekaru 15, sai ta ce za ta buɗe Facebook a March, 2012. A nan ta samu damar haɗuwa da abokan karatunta, da abokan wurin aiki, a cikinsu ta haɗu da wani abokinta tun suna ‘yan shekara 12, sun taɓa haɗuwa shekaru 20 a baya; suka ƙulla alaƙar soyayya (a Facebook), suka ci gaba da mu’amala (alhalin tana gidansa na aure)...” *
Gaskiya a yau muna wani irin zamani, da abu ne mai wahala, hana wani amfani da sabuwar fasaha, don ba shi ne mafita ba, duk don gudun lalacewar da ke ciki. Media ta zama tamkar wani sashe na rayuwar duk mai rayuwa a ƙarni na 21. A nan gaba ma a makarantu, zai zama dole a sa darussan ‘digital literacy.’
Sai dai mu yi amfani da fiƙhun Imam Aliyu رضي الله عنه na cikin Ighathat Al-lahfan 2/265, cewa, muna wani zamani, da ba irin na jiya ba ne, tarbiyyar al’umma da tunaninsu, na tafiya daidai da zamani ne.
Wani duba kuma, kowanne mutum mai amfani da waya (smartphone) yana da sirri, mace ce ko namiji, yaro ko babba. Idan kuma ka ce za ka riƙa bibiya, me wani ke yi a media, nan ma ranka ne ɓaci zai yi. Sai dai mu yi duba da wata ƙa’ida, An-Nawas bin Sam’an رضي الله عنه, ya ce; Manzon Allah ﷺ na cewa:
البر حسن الخلق، والإثم ما حاك في نفسك وكرهت أن يطلع عليه الناس
“Ɗa’a, ita ce kyakkyawar ɗabi’a, zunubi kuma shi ne (aikata wani) abin da yake ma ƙaiƙaiyi a zuciyarka, (har ba ka son mutane su sani (kana rufewa)” (Muslim, 2553). A ruwayar Wabisatu kuma, “duk abin da za ka riƙa ɓoyewa, ko ka ke kokwanto a kanshi…”.
Duk abin da za ka ji tsoro, har kake ɓoyewa, na wata mu’amala, ko ka yi ƙarya don rufe alaƙa da wani, haƙiƙa akwai zunubi, akwai cin amanar kanka, da ta iyayenka, ko abokanka (na aure), ga laifin ƙarya, da rashin kwanciyar hankali (agoraphobia).
Abin da ya sa abin ya fi ma zama ‘worse’ ga mata, babu namijin da zai yi alaƙa da mace, ba tare da amincewarta ba. Su ma mazan, su yi wa kansu nasiha, su kame kansu, su ji tsoron Allah, komai ka shuka, shi za ka girba.
* Rubutawa:
✍️ Ukasha Ismail
Fassara da kuma ƙari:
✍️ Aliyu M. Ahmad
5th Rabi’ul Awwal, 1444AH
1st October, 2022CE
#AliyuMAhmad
#FasaharZamani
#RayuwaDaNazari
0 Comments