Bashi (Ad-dayn)


Wani salon karɓa da biyan bashi a wannan zamani, kafin a karɓi bashi, mai karɓar bashi (madyn/debtor) zai yi ta ƙorafin yana cikin halin matsi, a taimaka masa. 

Shi ma mai bayar da bashi (daayin/creditor) kafin ya karɓo haƙƙinsa, sai ya yi ta lallashi da ƙorafi, da faɗar yana cikin damuwa ta rashin kuɗi, a dawo masa da kuɗinsa. Haka ma idan aikin ƙarfi ko wani 'services' mutum ya yi ma wani. 

Wani saboda ka nuna kana son haƙƙinka, har sai ku sami matsala, yana ma kallo maras mutunci, ya manta halas da aka masa.

Karɓar bashi a Shari'a, halas ne! Sai dai, a Shari'ah, yana da ƙa'idoji, ana duba rukunai: mai bayarwa, mai karɓa, abin bayarwa (kuɗi, kaya ko aiki), lokacin biya da kuma rubutu. Hatta a tsarin zamani, akwai dokokin da ake ɗankafe da harkokin bashi, mis. Limititation of Actions Act (2004), da Money Lenders Act...

1. Ba a karɓar bashi, har sai in ya zama dole (mis. abinci, ko gyaran muhalli na dole), mutum ya rasa yadda zai yi, saboda babu (Fath al-Baari, 4/547).

Haramun ne a karɓi bashi da ƙarya, a kuma karya alƙawari, a yi jinkirin biya (Bukhari, 832).

Idan kuma mutum aiki ya ma, wajibi ne ka biya shi haƙƙinsa, tun kafin guminsa ya bushe, kafin ya fara ƙorafi (Ibn Majah, 2537). 

2. Ba a bayar da bashi, ba tare da an yi rubutu ba bisa yarjajjeniya ba; misali, a rubuta:

"A yau ranar Lahadi 7th Rabi'ul Awwal, 1444AH (2nd October, 2022CE), 'X' ya karɓi rancen (bashin) kuɗi ₦100,00 a wajen 'Y' da niyyar zai dawo masa da shi a ranar Juma'a 12th ga Rabi'ul Awwal, 1444AH".

Mai bayarwa ya sa hannu, mai karɓa ya sa hannu. Ko a rubuta a 'record book' na masu karɓar bashi, ko a sa shaidu mutum biyu maza adalai, ko namiji 1 da mata 2 [Al-Baƙara, aya ta 282].

Idan kuma babu shaidu, babu abin rubutu, sai mai karɓar bashi ya bayar da jinga (collateral) na wani abu, idan kuma ka amince da mai karɓa, sai shi kuma ya cika alƙawari [Al-Baƙara, aya ta 283].

Wannan umarnin Allah ﷻ a cikin Alƙur'ani, don kar a saɓa yarjajjeniyar karbar bashi.

3. Hatsarin ƙin biyan bashi yana da yawa, daga cikin, akwai wani hadisin Muhammad bin Jahash رضي الله عنه, cewa; wata rana Manzon Allah ﷺ na zaune tare da sahabbai, sai aka ga ﷺ Ya ɗaga kansa sama, Ya jijjiga, Ya ce, "Subhanallah... na rantse da Ubangijin da raina ke hannunsa, inda mutum zai fita Jihadi, a kashe shi, a dawo masa da ransa, ya sake fita jihadi, a sake kashe shi, ba zai shiga Aljannah ba matuƙar akwai bashin da bai biya ba a kansa (An-Nasaa’i, 4367).

Ibn Muflih Al-Maqdisi (710 - 763 AH) a cikin al-Adaab al-Shar’iyyah (1/104); akwai mutumin da ya rasu, Manzon Allah ﷺ Ya ƙi sallatar gawarsa, saboda ana bin sa bashi. Manzon Allah ﷺ Ya ambaci cewa, duk mutumin da ya mutum ba ya girman kai, cin amana ko yaudara, ko ya mutu ba bashi a kansa, zai shiga Aljannah; akasin haka kuma, na hana mutum shiga Aljanna (Tirmidhi, 1572).

A cikin رياض الصالحين Imam An-nawawi ya kawo wani hadisi na Imam al-Bukhari (1587); cewa, Annabi صلى الله عليه وسلم ya ambaci wasu mutum 3 ba-Shi-ba-su a ranar tashin Alƙiyama, cikin har da wanda yake hana waɗanda ya saka aiki, ya hana su haƙƙinsu. "ورجل استأجر أجيرًا، فاستوفى منه، ولم يعطه أجره‏". 

4. Idan mutum ya mutum ya mutu ana bin sa bashi, ko gadonsa ba za a raba gadonsa ba, har sai an cire bashin da ake bin sa, an biya (Suratul Nisa'i, aya ta 11).

Idan ma abin da ya bari bai kai a biya bashin ba, dole ne magadansa su haɗa, su biya.

5. Idan mutum ya karɓi bashi kuma yana halin matsi, sai ya yi bayani kafin lokacin da aka ambata za a biya. Shi kuma mai haƙƙi, ya ji tsoron Allah, ya tausaya ya amince a jinkirta lokacin (Al-Baqara, aya ta 280).

Idan kuma ma, mai bayar da bashi (creditor) yana da yalwa, ya kuma ga mai karɓa ba zai iya biya ba, zai iya yafe masa (Al-Baqara, aya ta 280).

6. Idan mutum ya ci bashi ya kasa biya, akwai addu'ar da Manzon Allah Ya koyar, don neman agajin Ubangiji, duba Hisnul Muslim, addu'a ta 41:136 -7:

اللهم إني أعوذ بك من الهمِّ والحزن، والعجز والكسل، والجبن والبخل، وضلع الدَّين، وغلبة الرِّجال

Ma'ana: "Ya Allah! Ina neman tsarinka daga ƙunci, da baƙin ciki, da kasawa, da lalaci, da rowa, da tsoro, da NAUYIN BASHI, da rinjayen mazaje." (Abu Dawud, 1555).

7. Duk mutumin da ya ɗauki bashi ya baka, haƙiƙa taimaka maka ya yi, ba kuma lalle don yana da shi ne ya ɗauka ya ba ka ba, wani ma wataƙila buƙatarsa da kuɗi ta girmi taka, amma ya danne ya ba ka.

Idan ɗan kasuwa ne ka karɓi bashinsa na alal misali ₦10k na tsawon sati, ko wata; mu sani, wannan ₦10k a hannun ɗan kasuwa a cikin sati darajarta ƙaruwa za ta yi zuwa ₦12k, ko ₦15k... idan ya juya. Ka yi ƙoƙarin biyansa a kan lokaci.

A hadisin Buraydah ibn al-Aslami رضي الله عنه, Manzon Allah ﷺ Ya yi wa mai bayar da bashi ga mutumin da ya shiga ƙunci da albishirin samun LADAN SADAKA, haka shi ma wanda aka masa halacci, ya biya bashin da ake bin sa cikin sanyin rai, za a ba shi LADAN SADAKA (Ibn Majah, 1977).

A wani hadisin kuma na Abu Hurairah رضي الله عنه, Manzon Allah صلى الله عليه وسلم  ya ce: "Rashin biyan bashi (a kan lokaci) ga mutumin da ke da halin biya, zalunci ne."  Bashi ba ƙaramin abu ba ne, ya kamata mu hankalta.

✍️Aliyu M. Ahmad
7th Rabi'ul Awwal, 1444AH
2nd October, 2022CE

#AliyuMAhmad
#RayuwaDaNazari
#Bashi

Post a Comment

0 Comments