'Yan Samari: Emotional Intelligence

 

A matsayinka na namiji, abu ne mai kyau ka iya sarrafa kanka a kan komai, ka kuma fahimci abin da ke kewaye da kai, da yadda za ka yi mu’amala da su cikin ruwan sanyi, ba tare da cutar da kanka ko waninka ba. 

Akasin iya sarrafa kai, na iya sa ka samu naƙasu a rayuwa ta ɓangarori da dama, musamman a kan MACE. A kan mace (Iqlimiyya) aka fara babbar kaba’ira (kisan kai) a bayan ƙasa, tsakanin Ƙabila da Habila (Al-Ma’idah, 5:27).

Ita kuma wannan SOYAYYA, muna ganinta kamar ba komai ba, amma tana daga cikin abubuwan da ke sa rashin maida hankali kan ƙalubalen rayuwa muhimmai, musamman ga ‘matashin namiji’. 

1. Idan ka san ba ka shirya AURE ba, ka ajiye batun neman soyayya a gefe, ka yi ƙoƙarin gina kanka tukun, ‘no matter what you feel’, wannan shi ne babban 'jihadin' da za ka yi wa kanka. 

A shari’ah, ana gina soyayya tsakanin namiji da mace ne da manufar zama tare har abada (aure) ‘لم نر للمتحابين مثل النكاح’ [Ibn Majah, 1847]. Dole ka koyi rintse ido, da sarrafa kanka da sha’awarka.

A shekarun samarta, duk abin da ba shi da manufa, barinsa shi ya fi, ka fuskanci abin da zai gyara gobenka, ba ruguza ma mafarki ba.

Soyayya tana zuƙe lokaci, kuɗi, kulawa, tunani, jajircewa... duk ka bayar wa soyayya su, a ƙarshe, ba za ka sami abin da kake so ba, kuma ka yi asara. Duk soyayyar da bata da manufa, ɓatawa juna lokaci ce.

Allah (SWT) na cewa:

وليستعفف الذين لا يجدون نكاحا حتى يغنيهم الله من فضله

Ma’ana: “kuma waɗannan da ba su samu (damar) aure ba, su kame kansu, har sai Allah Ya wadatar da su daga falalarSa.” [Nur, aya ta 33].

2. Idan kuma ka nemi soyayya (koda da niyyar aure ce), sai kai tsaye mace ta ƙi amince ma, ka yi Hamdala, Allah ya so ka da rahama. 

Ka fahimta, a nuna an ƙi ka kai tsaye, ya fi alheri ka kasance cikin rataya (Bature na ce wa: “a clear rejection, is better than fake promise”). 

Akwai labarin Mugheeth, sahabin Annabi ﷺ, ya so wata mata; ‘Barira’, matuƙa, wanda har ta kai su ga aure, amma ita ba ta son shi, har kuka yake a kanta; Manzon Allah ﷺ ya ce masa ya haƙura (Bukhari, 5283). Shaykhul Islam ibn Taymiyya رحمه الله na cewa; “duk wanda aka jarraba da soyayya, ya kiyaye mutuncinsa, ya yi haƙuri, Allah zai bashi ladan masu haƙuri” [مجموع الفتاوى، 10/133].
 
3. Idan aka nuna ba a sonka, kai kuma ka nace, to a nan; mace za ta kula ka, don kar ka ce tana wulaƙanta ka, amma “sure you, you would never be loved”; Kar ka cutar da kanka da ‘one side love’ (soyayyar ɓangare ɗaya); daga ƙarshe ma, za a ma ‘constructive dismissal’, kana ta wahalar da kanka da ɓatawa kanka lokaci, maimakon sadaukar da tunaninka don ka gina kanka, ko neman wata soyayyar. 

4. Kyautatawa tana daga cikin ginshiƙan tabbatar da soyayya, amma ka bi a hankali wajen ɗawainiyya wa soyayya. Kar yi wa soyayya hidima ta mantar da kai shirin aure, kuɗaɗen da kake samu, kullum suna ƙarewa a ‘recharge cards’ da kuɗin anko da maƙulashe, ko ɗinke-ɗinke don yi wa ƙauna kwalliyya; da wannan ‘pseudo-capacity’,  kana ji, kana gani, wani (late comer’ ever ready) zai zo ya aure ta, don abin da ya kamata ka tara, ka yi aure, ka kashe mata shi, budurwa ta cinye.

5. Idan ka tarar mace da wani saurayi an yi mata baiko, haramun ne ka yi nema a kan nema, domin hakan na jawo gasa, fitina, munafurci, wasiwasi da rashin kwanciyar hankali tsakanin masoya, da ƙarya [Bukhari, 5142].

Idan kuma ba a yi baiko ba, tom akwai aiki a gabanka. Idan ka yi sa’a ta karɓi soyayyarka, ba wai kana zuwa rana ɗaya za ta daina son wani ta so ka ba; soyayya ba kamar rigar sawa ba ce, da za ka iya cire wa, da sa wa, a duk lokacin da ka so, a’a; abu ne da zuciya ce kaɗai ke iya fayyace ya ake ji. 

Idan ka tarar mace tana soyayya da wani saurayi, ko tana da ex(es), ko tsohon miji, zai yi wuya ta iya manta da waɗannan, saboda sun taɓa ba ta farin cikin a baya. Sai dai, ya danganta da wane irin rabuwa suka yi. Sonsu kuma a zuciyarta, ba zai fice baki ɗaya ba, sai dai yana raguwa, saboda samunka.

Kar ka damu da wannan, aikinka a nan shi ne, ka yi ƙoƙari maye gurbin wancan da kulawa, da sa ta farin ciki...

6. Babu macen da za ta iya tsayawa da saurayi guda ɗaya, “no matter how innocence she looks”, kar ka cutar da kanka duk da addinance ma, ‘double dating’, yana kai mutum ga yawan ƙarya, da rashin kwanciyar hankali. Ai ita mace, ce wa ake ana son ta, ba wai ita ke ce wa tana so ba (don kar ta wulaƙanta mutane).

Sai dai, a ɗabi’ar mace, kamar yadda masana halayya suka faɗa, Tina B. Tessina da Laurel House, takan iya tara samari da yawa, ta yi soyayya da su a lokaci guda, amma a haƙiƙa guda ɗaya take so, duk sauran burge ta kawai suke. 

Wani kwalliyarsa ke burgeta, wani sarrafa kalamai masu narkar da zuciyarta, wani barkwanci, wani jigila akan al'amuranta ya sa ta ke kula shi, wani... amma ɗayan can dai take so da gaske.

Kar ka damu don budurwarka na kula wasu, idan da gaske aurenta za ka yi, to ka dai tabbatar shin kai ne na ƙarfe, ko na jabin ne? Don kar ka ɓatawa kanka lokaci. Kar kuma ka zama lusari, kana nuna rashin kishi, a'a; ka ƙara jajircewa, don kar a kada kai, komai kusancinku da mace.

Idan ka ce za ka ɓata ranka kan tana kula wani (idna dai ba aurenta ka yi ba), har ka yi fushi, a lokacin za ta jawo wancan, ya ba ta farin ciki.

7. Ka fahimci ‘transferring aggression’, yanayi ne da mace ke shiga a lokacin da wani ya ɓata mata rai, misali; a gida, abokanta ko wani saurayin ba kai ba. 

Idan ka je wajen mace, ka tarar ranta a ɓace, kar ka yi gaggawa jefa kanka cikin damuwarta, wata kan iya dawo da ɓacin ran kanka, wata kuma kan iya ɗana ma tarkon roƙo ko ɗora ma wani nauyi da ba za ka iya cire kanka ba, kamar anko, ko kuɗi, ko dai wata buƙatar.

10. Ba cinyewa ba ne, tara ‘yan mata’; kowacce kala ka gani, sai ka tare ka karɓi lambar waya, wai kai gaye; lokaci da himmar da za ka ɓata wajen hira, ko hidimar wa mata, ya cancanci ka ba wa wani abu da zai gina ka, ka zama mutum.

✍️ Aliyu M. Ahmad
4th Rabi’ul Awwal, 1444AH
30th September, 2022CE

#AliyuMAhmad 
#RayuwaDaNazari

Post a Comment

0 Comments