'Yan Mata A Kama Sana'a


‘Yar uwata II

Ki ajiye girman kai, ki dubi yanayin gidanku (ba yanayin  gidan su ƙawayenki ba), ki kama sana’a don rufawa kanki asiri, kar ki tsaya jiran tsammanin daga samari, yayye, uncles, cousins… kina ta kumbura, wai ana miki rowa, wai no ƙi taimaka miki. 

Akwai sana’o’i da yawa da mata za su iya daga gida, cikin mutunci, kamar; kasuwanci (siyar da sutura, kayan kwalliya, kayan amfanin gida…), dillanci/haɗin gwuiwa (affiliated marketing), ɗinki, saƙa, kitso da gyaran gashi, henna/ƙunshi, makeup, snacks (maƙulashe), pastries, drinks, kiwon kaji/awaki… da iliminki, har ajin koyar da yara za ki iya buɗewa, kina koyar da su lissafi, languages, ko kimiyya ana biyanki. Mutunciki, sana’arki! Sana’ar mace halal ce, Nana Khadija bint Khuwaylid رضي الله عنها misali ce ga mata.

---------------------------------------
ZA KI MA IYA FARA SANA’A, 
BA TARE DA SISINKI BA

1. Bay’ul Salam
Akwai wacce na taɓa tambaya ta shawara fara sana’ar ‘awara’, kuma ba ta da jari. SHAWARA NA BATA, BA JARI BA. Na yi mata flier na tallar, a yi ‘placing order with payment’, kafin kwana biyu, aka tara mata kuɗi, ta siyo kayan haɗin awara, ta yi, ta cire riba (ta samu jarin da take juyawa), aka zo, aka karɓa, wasu aka musu delivery. WANNAN YA HALLATA A MUSULUNCI, shi ne BAY’UL SALAM (Bukhari, 2240 & Muslim, 1604).

2. Affiliated Marketing (haɗin gwuiwa)/Dillanci
Za ki karɓo tallatar kaya a shagon yayanki, ko wani; ki tallata, a siya, ya biya, matuƙar babu  kar ki yi ‘tawliyah’; wannan shi ne ‘samsarah’ (dillanci). Ko ki karɓo, ki siyar, ki maida kuɗin. 

Amma babu kyau, kin a tallatar kayan da baki da shi, sai in ana so tukun ki hau nema, wani lokacin, abin da kika tallata daban, wannan kika deliɓery daban, wannan haramun ne (Abu Dawood, 3499).

3. Bashi ko Yarjejjeniyar Haɗin Gwuiwa
Za kiya karɓar bashin kuɗi a gida, da niyyar za ki mayar bayan zuwa wani lokaci, kin juya kuɗi, da sharaɗin ba ruwa a ciki (Al-Baƙarah, 275). Misali, za ku iya yin ‘mudharabah’ ko ‘musharaka’, ko a siyo miki kayan fara sana’a, ki juya, ki haɗa kuɗin daga baya (murabaha).

4. Ki nemi a tallafa miki, za ki fara sana’a
Ba aibu ba ne, don kin nemi mahaifinki, ko wani ɗan uwanki ya tallafa miki da jari.
 
Sai dai wani lokacin kuma, gaskiya ana ƙorafi da ku, ƙanwata; za a ba ku kuɗi don ku ja jari, amma da zarar wani biki ya gifta, sai kuɗi ya tafi a ashobe (anko), jari ya karye. Biki ya wuce, ya bar wawa da susar ƙeya.
---------------------------------------

Bar ganin kanki a babbar yarinya, IDAN BA KI NEMAWA KANKI TA SANA’A BA, ZA KI ROƘA, roƙon kuma ƙasƙanci ne. Muna wani zamani da ba kowanne mutum ne zai iya dunƙule kuɗi ya baki haka kawai don buƙatarki ba, ba tare da kin tambaya ba, ko ba tare da wata alaƙa tsakaninku ba. 

Yanzu kuma! Iyaye kuma, ƙoƙarinsu a rufawa gida asiri, a samar da abinci da sauran buƙatun dole ne a gabansu. Yayye maza kuma, don Allah, ko rabin abin da kuke kashewa ‘yan mata, ku riƙa tallafawa ‘yan uwanku mata (yayye/ƙanne), ba iya abinci ne kurum ake buƙata ba, akwai sauran buƙatun mata.  

✍️Aliyu M. Ahmad
15th Safar, 1444AH
12th September, 2022CE

#AliyuMAhmad
#RayuwaDaNazari
#Sanaa #Yaruwata

Post a Comment

0 Comments