Pi π


Ba na yi wa 'yan Pi π nasiha ba, kar ta fashe, a ƙi turo min kasona, amma dai akwai buƙatar mu tunasar da kanmu.

Har yanzu, darajar Pi π bai gama karɓuwa a kasuwar duniya ba, ma’ana, ba a iyankance masa daraja ba. Su Dr. Chengdiao da Dr. Nicolas Kokkalis su gama arzikinsu, da engagements da traffic, ga 'data' na mutane da suka tara.

Pi π: 
1. Ta iyu ya zama gaskiya, ya kai darajar da ake kirdado, 
4. Ko ma ya wuce darajar da ake kirdado, 
3. Ko ya gaza darajar da ake kirdado, 
4. Ko ma ya yi failing (ba a fatan haka). 

* Ba wanda zai ce ma akwai tabbas, ba wanda zai ce ma babu tabbas, ana dai tsammani ne.

Amma dai burin da ake sa wa a kan Pi π, ya wuce tunani, duk ‘pseudo-reality’ ne, ana jiran tsammani, har tsammanin na neman taɓa tunanin wasu mutane da yawa.

Wannan jajircewar, da imani da ghaibu ga Pi π, shi ne irin ‘ijtihadin’ da ake son mutum ya yi a duk wani lamari na rayuwarsa domin ya kai ga nasara. Da a ce a wani kasuwanci na dahir aka sa wa irin wannan 'effort' ɗin, tabbas tsawon kwanakin da aka fara Pi π, da labari ya sha-bamban. 

Ƙaddara darajar Pi π za ta zo a miliyoyin kuɗaɗe, ina da tabbacin, kaso 80% – 90%, nan da shekaru biyar za su ƙara faɗawa matsanancin talauci, me ya sa? A tunani da furuci, 'liabilities' mutane za su ƙarawa kansu.

Akwai wata muƙala da Ayobami Sanusi (July, 2022) ya rubuta a shafin jaridar Tribune, kan dalilan da ya sa talaka ke dauwama a talauci guda 5:

1. Ba ya ƙoƙarin nema da kansa
2. Yana jiran wani ya zo ya ba shi
3. Ba ya tafiya da sauyin zamani
4. Bai san ya juya kuɗi ba, ko ka ba shi, kashewa zai yi
5. Ba ya duban wata dama ta samun kuɗi, sai dai ta kashe kuɗi

Percy Bysshe Shelley (1792 – 1822) ma ya faɗi makamanciyyar wannan a “A Defence of Poetry” (1840). Saboda a irin tunanin waɗannan, arziki shi ne kuɗi da kayan ƙawa (luxuries).

Idan ka sami matalauta kamar mutum 100, ka raba musu Naira miliyan biyar-biyar (₦5m), bayan shekara biyar, da wuya ka sami kaso 10% daga cikin 100% nan da za su yi amfani da kuɗin wajen juyawa, su ci gaba. Sauran 90% ɗin, sun sa yi gida, abin hawa, sutura, latest devices… sun dai kashe kuɗin, sun huce haushi da luxuries. Misali, a binciki waɗanda suka sami lamunin NISAL: 500K, 750k, 1m… shi ya sa Sunday Adelaja (2017) ke cewa: “Talaucin gaskiya, a tunani ne, ba a aljihu ba.”  

A rage buri, a maida hankali kan nenamn kuɗi mai dahir, sannan a ci gaba da mining, Allah Ya sa ta fashe, ya kuma yi daraja.

✍️ Aliyu M. Ahmad
17th Safar, 1444AH
14th September, 2022CE

#AliyuMAhmad 
#RayuwaDaNazari
#FasaharZamani #Pi

Post a Comment

0 Comments