Tashi Ka Nema, Allah Zai Ba Ka


ARZIKI
Nema ne namu, arziƙi kuma na Allah ne. Matuƙar za ka fita ka nema, Allah zai rufa ma asiri (Al-Juma'a, 62:10).

SHIRIYA
Tarbiyya ce tamu, shiriya ta Allah ce. Duk mai neman shiriya, Allah zai shiryar da shi (Al-Baqara, 2:76 - 79).

Duk mai bada tarbiyya, ya yi ƙoƙarinsa, ya dogara da Allah, Allah zai shiryar masa zuri'a (Luƙman, 31:12-19).

TSARO
Tsarewa ce tamu, tsaro kuma na Allah ne. Duk wanda ya ɗauki matakan kariya, ya kiyaye, ya tsare, Allah zai ba shi tsaro (Yusuf, 12:64).

NASARA DA RABO
Jajircewa ce tamu, nasara da rabo da ɗaukaka duk na hannun Ubangiji. Ɗaukakar ba ruwanta da nasaba, wayo ko dabara, Allah ke ba wa wanda ya so, ka nema a wajen Allah (Ali-Imran, 3:37).

LAFIYA
Kiyayewa ko neman magani ne namu, amma lafiya ta Allah ce (Al-Anbiya'i, 21:83-84).

Rahamar Allah ce, duk wanda ya jajirce, Ubangiji zai ba shi nasara, da Musulmi, da waninsa. Jarrabawar Ubangiji ce, ya jarrabe ka da ƙasƙanci a duniya, idan ka yi haƙuri, ka tadda rabonka a lahira.

A cikin Alkur'ani, Ubangiji Ya umarci Annabawa da salihan bayi عليهم السلام da jajirce a wurare da dama; misali: Anqabut (29:69), Ali-Imran (3: 102 & 133), Al-Muzammil (73:1-10), Maryam (19:12) da sauransu.

Rufin asiri da wadatar zuci ne manufar, tara dukiya wani abu ne na daban. Lafiya, kwanciyar hankali, kuɗi, shiriya... duk arziƙi ne. Ka zama tsuntsun, ka dogara da Allah, ka tashi ka nema, Ubangiji ba zai kunyata ka ba.

✍️Aliyu M. Ahmad
15th Safar, 1444AH
12th September, 2022CE

#AliyuMAhmad
#RayuwaDaNazari

Post a Comment

0 Comments