Mutum mai hankali, shi ne wanda ya san abin da ya kamata ya furta na magana. Koda maganar ilimi ce! Mutum mai tunani, shi ne wanda yake auna, me ya kamata ya furta na magana, ko ya yi shiru (saboda gudun abin da zai je, ya zo).
Shiru (silence) alkhairi ne! Gwamma a ce, BA KA CE BA, da a ce, KA CE. Yawan suturu kan bayyana tsiraici na asirin da shiru ya rufe (na rashin sani).
Ba a ce ba ka yi karatu ba (amma wanne ɓangaren?) Nkem Okoh (2008) a Preface to Oral Literature; AFP Onitsha; ya ambata, bambacin adabin zube (literature of power) da adabin ilimi (literature of knowledge), ko da a wajen tawili (interpretation) da tarke/naƙadi (criticism) akwai bambanci.
A tarken adabin zube, akwai nazariyyat (theories) tenants, frames, concepts, principles, constructs… daga mazhabobin ilimi, nazari da tunani na Formalism, Semiology, Psychoanalysis, Marxism, Structuralism, Feminism, Modernism…, idan wani ya yi rubutun zube, sai ka ɗauko fatawowin John Dryden, Roland Barthes, I.A. Richards, P.R. Leavis, Eliot, Mathew Arnold, Hulme, William Empson, C. Caudwell, John Crowe, Zellig Harris, Pustejovsky, Stubbs, Philip Sidney, Johann Wolfgang, Sigmund Freud, William Wordsworth... ka yi framing, tukun ka fidda fahimtarka; shi ma ba da molanka ake fassarawa.
Ba za mu fassara ayoyin Alƙur'ani kai tsaye ba, don mun iya Larabci, ko karanta Tarjama kaɗai; Ubangiji ya yi maganar ‘tawili’ a Ali-Imran (3:7); mafi sauƙi, cikin Alƙur’ani, wasu ayoyin ke fassara sashe (تفسير القرآن بالقرآن), akwai kuma 'nasikh' da 'mansukh'.
Idan muka ɗauko ayar Bakara (2:62) Ma’ida da (5:69) ka haɗa da ayoyin cikin Ali-Imran (3:85 - 86) Ma’ida (5:59) da A’araf (7:50) da al-Bayyinah (98:6); ilimi ne zai warware ma, ba ka ɗauko ɗaya, ka yi hukunci da ita, daidai da ra'ayinka ba.
Sannan ‘nasaba’ ba ta da alaƙa da imani, ko sakamako; akwai misalin makusantan Annabi Ibahim, Nuhu da Lut; iyayen, ‘ya’ya da matan aure: a Maryam (19:42 - 48), Hud (11:36 - 48), da Al-Hijr (15:60) da sauransu; ko a wajen ceto, sai wanda ya yi imani, aiyukan zunubai suka kai wuta za a ceta, ba mai shirka ba (Muslim, 1577).
Akwai lokacin da malam ya ce min, "hatta littafin da ba a gaban malami ka koyi shi ba, kar ka karantar wa wasu shi, domin wata fassarar ba iya iya yare ba ce, sai daga ‘arifai’, masana karatun na haƙiƙa. Akwai fassara ga jinsi, akwai fassara ga shekaru, akwai fassarar da ake a muhalli... wata fassarar kuma, yau-da-gobe, yawan shekaru, da waƙi'in rayuwa ne za su tabbatar ma da fassara.
Ina yi wa kaina da mu nasiha, addini ba molanka ba ne, ko yadda ya zo mana tunani. Mu koma gaban malamai, mu ɗauko ƙaƙanan littafan aƙida da fiƙhu... nan da ƴaƴanmu da ƙannenmu ke koyo, a biya ma. Sai an yi karatu, ake ibada, sai an yi karatu, ake magana kan addini.
Idan kuma muna jin ƙaiƙayin maganar ilimi, ai mun yi karatu; a fannoni kimiyya, ko fasaha, ko yare, ko tattali, ko yanayin ƙasa da zamantakewa; mu taƙaita kan inda muka fi kwarewa, mu amfanar da al’umma da shi; ɓangaren addini, mu bar wa masana fannin.
A ƙarshe, wuta ko aljannar wani ba ta shafe mu ba, mu mayar da hankali ga tamu lahirar, Allah Ya datar da mu!
✍️ Aliyu M. Ahmad
25th Safar, 1444AH
22nd September, 2022CE
#AliyuMAhmad
#RayuwaDaNazari
0 Comments