Abu Muhammad Sulaiman bin Mihran Al-A'mash (61 - 148AH) yana daga cikin malaman Imam Abu Hanifa, da Fudail bin Iyad da Sufyan Al-Thawry رحمهم الله, ya ce:
"Wata rana muna tare Ibrahim An-Nakha'i, ya jiyar da ni hadisai guda 6, na haddace su (a kaina). Bayan na dawo gida, sai baiwata ta ce: "Ya ubangijina! Babu garin alƙama a gida." Jin wannan, ya sanya na mance duk hadisai 6 da na haddace."
Akwai wata addu'a da Manzon Allah ﷺ Ya koyar cikin Zikiri Safiya da Maraice, ta neman tsari da kafurci, talauci da azabar ƙabari, (tana cikin Hisnul Muslim, addu'a mai lamba 82)
اللهم إني أعوذ بك من الكفر والفقر، اللهم إني أعوذ بك من عذاب القبر
Sau 3 da safe, 3 da yamma.
Bin Abi Bakrah ya ce, ya ji daga babansa, cewa; Manzon Allah ﷺ Yana karanta wannan addu'ar a ƙarshen kowacce sallah (Sunanun Nasa'i).
A ƙarshe, idan Allah Ya baka hali, ka yayewa makwaftanka, abokanka da 'yan uwanka na jini ƙunci, matsi da yunwa; ka yi nazari kan yawan rafkanuwa da limamin masallacinku ke yi... Allah zai Ya ye ma ta ka damuwar a ramko (Muslim, 2699).
✍️ Aliyu M. Ahmad
24th Safar, 1444AH
21st September, 2022CE
#AliyuMAhmad
#RayuwaDaNazari
0 Comments