Kalmar 'JAHILCI', Larabci ce;
'RASHIN SANI' ita ce Hausa.
Kalmar 'ILIMI', Larabci ce;
'SANI' ita ce Hausa.
Kalmar 'ARZIKI', Larabci ce;
'WADATA', ita ce Hausa.
Kalmar 'ÆŠALIBI:, Larabci ce;
'MAI KOYO', ita ce Hausa.
Kalmar 'MALAMI', daga Larabci ce (mu'allim);
'MAI KOYARWA', ita ce Hausa.
Kalmar 'TARBIYYA', Larabci ce,
'RAINO/HORO' ita ce Hausa.
Sauran misalai 👉
• Imani = yarda
• Ibada = bauta
• aibu = laifi
• mashahuri = sananne
• adalci = daidai
• bawali = fitsari
• É—ahara = tsarki
• baras = kuturta
• rahusa = sauÆ™i
• kalami = magana
• wasiwasi = kokwanto... dss.
Tasirin addinin Musulunci da adabin Musulunci ya sabbabawa harshen Hausa aro (loanword) daga Larabci, akwai kuma wasu kalmomin da aka maye su da na Larabci (replacement) musamman don sayewa; misali: al'aura/tsiraici, rih (iska)/tusa, mutuwa/rigaya...
Misali, tasirin kalmar JAHILCI daga cikin Alƙur'ani, idan aka yi amfani da ita kan mutum, ya fi jin zafi, fiye da a ce 'BAI SANI BA', a ma'anar, duk ɗaya ce; bambancin harshe ne.
Akwai kalmomin da suka ɓace, saboda yawan amfani da na Larabci; mis. amfani, haƙƙi, lissafi (hisab), ɗabi'a, halayya, mutuwa (fakuwa/rasuwa), mulki (siyasa)/jagoranci, attajiri/ɗan kasuwa... (ni dai ban san kalmominsu (na wasu daga cikinsu) na Hausa na asali ba).
Akwai kuma sabbin kalmomi na baƙin abubuwa (na ibada, mulki, abinci da sutura) waɗanda a da a Hausawa ba su da shi; misali: liman (imam), aya, surah, zakkah, halal, haram, bindiga, sukari, jami'a, alƙalami, alƙali, hukuma, hakimi, diyya, haraji, tufa, inibi, nahwu, jihadi, alkibla, sufur (zero), aljihu, alkaki, albasa, alkama, alewa, almakashi... da sauransu.
Aron kalma daga wani yaren ba aibu ba ne, babu yaren da ba ya aro; kamar harshen Turanci (English) ya fi kowanne yaren duniya aron kalma, daga Latin, French, Greek, Germanic... (Algeo, 1999). Larabci shi ne yaren da ya fi kowanne yalwar kalmomi, amma ya aro kalmomi daga Latin, Greek, Persian, Syriac, Turkish da sauransu (Noor, 2015).
Akwai wani rubutuna na 2017 kan aron kalma (word borrowing) da kashe-kashenta a COMMENT SECTION 👇👇👇
✍️Aliyu M. Ahmad
25th Safar, 1444AH
22nd September, 2022CE
#AliyuMAhmad
#RayuwaDaNazari
#Linguistics #Hausa
0 Comments