Mutuwar Sarauniyya ta wuce wannan cecekucen da ake a social media, domin rayuwar Sarauniyya ta shafi rayuwarmu tun 1952 zuwa yau. A hannunta aka karɓa mana ƴanci (Nijeriya). Nijeriya ta zama 'reams' cikin mammobin 'Commonwealth' da ta ƙirƙira, rayuwarta da mutuwarta na da tasiri sosai kan adabi da harshen da ya fi kowanne harshe ƙarfi da yaɗuwa a duniyar yau (Turanci/English), rayuwarta ta taɓa al'adunmu, tsarin zamantakewarmu ci gaba da kwan baya a rayuwarmu.
Akwai littafai sama da 1000 da documentaries (misali, The Arrivals na Abdullah Hashim) kan tarihinta, tasirin rayuwarta ga ci gaban duniya, rikice-rikice da zaman lafiya, tattalin arzikin duniya... wannan duk ya shafi rayuwarmu, kar kace bai fashe ka ba don tana Ingila, kana Nijeriya. Ƙaramin misali, yanzu rikici ake tsakanin Russia da Ukraine, mu muna Nijeriya, amma muna ɗanɗana radadin farashin fulawa (flour).
Da za mu yi nazari, karatu, kan abubuwan da suka shafe mu game da Sarauniyya, wataƙila mu tsinci abubuwan da za mu gyara duniyarmu da lahirarmu da shi. Ko ba komai, mutuwar izna ce gare mu, da jagorori, duk daren-darewa, karfin iko da dukiya, kowa zai mutu, ya zama tarihi.
✍️ Aliyu M. Ahmad
12th Safar, 1444AH
9th September, 2022CE
#AliyuMAhmad
#AliyusLibrary
#RayuwaDaNazari
#QueenElizabeth
0 Comments