Jihar Jigawa, daya ce daga cikin sabbin jahoji 9 da aka kirkira a rana mai kamar ta yau, 27 ga watan Agusta cikin shekarar 1991 karkashin mulkin soja na Gen. Ibrahim Babangida, karkashin Kundin Kirkira da Canjin Tsarin Mulki na Soja (No. 37 na shekarar 1991). Jihar Jigawa, yanki ce daga tsohuwar Jihar Kano, kuma tana da fadin kasa murraba’i 22,410. Ta yi makwaftaka da Jihar Kano daga Yamma, Jahohin Bauchi da Yobe daga Gabas, Katsina da kuma Jamhuriyya Nijar daga Arewa.
Jihar Jigawa ta samo sunanta ne ‘Jigawa’ daga manyan-manyan ‘jigayi’ (tarin kasa, ko ‘hill’ a Turance) dake kan hanyar Jahun-Dutse. Wannan tarin kasar (jigawa) ya sa ake yiwa Jihar kirari da ‘Tarin Allah’. Ana kuma yiwa Jihar Jigawa take da ‘Sabuwar Duniya’ (The New World).
Yawancin mazauna Jihar Jigawa Hausawa ne, sai Fulani, Mangawa, Badawa da kuma Ngizimawa masu magana da harshen Kanuri. Sai kuma sauran kabilu (baki) daga wasu sassan Nijeriya da ma wajen Kasar. Yanwancinsu Musulmai, da kusan kaso 99% cikin mutum sama da miliyan hudu (4m) dake zaune a Jihar (NPC, 2016).
Birnin Dutse, shi ne babban birni Jihar (capital city), tare da sauran kananan hukumomi 27 (ciki har da Dutse), tana da gundumomin ‘yan majalissar dattawa 3, gundumomin ‘yan majalissar tarayya 11, da na majalissar jiha 30. Sai masarautun gargajiya 5, Hadejia, Kazaure, Gumel, Dutse da Ringim.
Jihar Jigawa na da arzikin kasar noma rani da damuna, kiwo da su (kamun kifi). Jigawa ita ce Jiha ta 5 a noman da fitar da shinkafa a duk fadin Nijeriya da samar da ton miliyan 2 da dubu dari (2.1m).
Alhamdulillah! A bangaren ilimi, Jihar Jigawa na da Jami’ar mallakin Gwamnatinta Tarayya (Federal Universty Dutse), Jami’ar Jihar (Sule Lamido University, K/Hausa), Hussaini Adamu Federal Polytechnic Kazaure, Jigawa State Polytechnic Dutse, Binyaminu Usman Polytechnic Hadejia, School of Nursing B/Kudu da Hadejia, JSCOE Gumel, JSCILS Ringim, Jigawa State Institute of Information Technology Kazaure, Khadija University Majia (Private), As-Salam Global University Hadejia (JIBWIS), NOUN Study centres, sai sabuwar Federal University of Technology, Babura da sauransu.
In karkare ma, iskar Jihar Jigawa na da dadin shaka, saboda karancin ‘magurbatun iska.’ Jihar Jigawa tafi kowacce Jiha a Nijeriya zaman lafiya, saukin rayuwa, da tarbiyya. Don a Jihar Jigawa ne zaka zo gari ka ga kowacce mace da hijiba (har karuwa), girmama manya, rike addini da al’ada. A Jihar Jigawa akwai karancin gidajen holewa da badala. Ka so zuwa ganin ginenen zamanin a Sakatariyyar Mulki ta Jiha, NYSC Camp, Airport, hasken titi (streetlight), hanyoyin sufuri. Da in zaka shigo Jigawa ta hanyar Kano, ko bacci ka ke sai farka, saboda canji, abubuwan sun yawa a rubutu…
Jihata, a bar alfaharina.
Allah Ya kara mana zaman lafiya da yalwar arziki.
© Aliyu M. Ahmad
27th August, 2021
2 Comments
Ameenn ya Allah. Allah shi cigaba da kare mana kasarmu Nigeria. Ameen
ReplyDeleteAllahumma amin,
DeleteJazakumullah bi khyrn