A nazarce, ba wata kalma ELITE a social media, sai dai INFLUENCER.
------------------------------
* Shiga 👉👉 https://bit.ly/ElitedaInfluencer domin karanta cikakken rubutu game da SOCIAL MEDIA INFLUENCER
------------------------------
Influencer shi ne mutum mai tarin mabiya a social media (followers), influencer ya karkasu zuwa yawan followers: mega (1m+), macro (40k – 1m), micro (1k – 40k), nano (mai followers kasa da 1k).
Elite a nazariyyar zamantakewa (sociological theory), rukuni ne na mutumin da suke riÆ™e da madafun iko (mulki), ko tarin dukiya. Ana auna matsayin mutum a ‘elite class’ da dukiya ko iko ne a rayuwar zahiri.
Zama influence a social media ba ya buÆ™atar kasancewa cikin rukunin ‘elite’ a zahiri, domin zuwan social media ya É—aga darajar waÉ—anda ba kowa ba, zuwa sanannu, saboda bayyanar wata baiwa da Ubangiji ya musu. Mai buÆ™atar ‘contents’ da kake wallafawa, zai bibiye ka.
Akan sami ‘elite’ influencer a social media (kamar ‘yan siyasa, malamai, mawaÆ™a, ‘yan film...), akan kuma sami waÉ—anda suke rukunin elite amma ba shi da influencing a social media. Sai dai ta É“angaren halayya, wani lokacin, influencer na nuna irin halin elite, “privileging”, ma’ana, nuna tausasawa da kulawa ga influencers ‘kwarya ta bi kwarya’ a alakar social media.
✍️ Aliyu M. Ahmad
8th Safar, 1444AH
5th September, 2022CE
#AliyuMAhmad
#RayuwaDaNazari
#FasaharZamani
#Influencer
0 Comments