Kuɗi, kuɗi... idanuwan da yawa sun rufe, kullum; maganar kawai, ya za a yi, a sami kuɗi; tauye mudu, zamba cikin aminci, cin amana, cin hanci da rashawa, sata, cin-da-addini, ci-da-ceto, riba, fasiƙanci… ba a kulawa da halal ko haram, kurum a sami kuɗi.
Abu ne mai kyau ilmantar da kanmu ilimin tsimi (tattali) na Muslunci (Islamic Financial Literacy) domin kaucewa shubuhu da haram ta kai tsaye, domin abin ci da sha, sutura, sautin sauraro, furuci… ba a iya a ci a ƙoshi, ko a yi kwalliya, a fito fes, ko jin sauti mai daɗi ba ne kurum, a’a; suna da matuƙar tasiri ga ruhinmu (soul), wannan na cikin ‘maƙasid’ na haramta haram.
Imam Al-Ghazali (448AH – 501AH) cikin Ihya ‘Ulum al-Din, 2/91, daga Sahal رضي الله عنه yana cewa:
“Duk wanda yake cin haram, sai gaɓɓan jikinsa sun saɓa masa, ko ya sani/so, ko bai sani/so ba. Haka nan, duk wanda abincinsa na halal ne, gaɓɓan jikinsa za su masa ɗa’a”.
Daga cikin illolin cin haram, za ka yi ta ƙoƙarin kaucewa aiyukan alfasha, amma ba za iya ba, saboda ka gina tsokar jikinka ko ta iyalanka da haram. ‘Ya’yanka za su iya fin ƙarfinka (saboda ka gina tsokarsu da haram). Ka yi ibada ko addu’a, a ƙi karɓa. A ƙarshe idan aka je lahira, sai ka yi bayani, kobo-bayan-kobo, a ina ka samo, a ina ka kashe su.
Wani abun haushi, yawanci ƙoƙarin tara kuɗi ta hanyoyin haram, ba ana yi ne don yunwar ciki ba, a'a; ana yi ne don gasa, a sayi lexuries don burge mutane, da rashin wadatar zuci har ya zamewa mutum jiki 'kleptomania' (Dillon, 2017)¹.
Ubangiji Yana rufawa bawa asiri koda ba Musulmi ba ne matuƙar zai ci guminsa, ya yi gaskiya da riƙon amana. Sannan, zunubin cin haƙƙin mutane idan ya yawaita, yana jefa mutane cikin ƙunci koda al’ummar Musulma ce, ka ga an sami gurɓatattun jagorori, rashin tsaro, tsadar rayuwa, taɓarɓarewar tattali da rashin kayan more rayuwa.
Allah Ya azurta mu da halal da wadatar zuci.
✍️ Aliyu M. Ahmad
14th Safar, 1444AH
11th September, 2022CE
#AliyuMAhmad #RayuwaDaNazari #HalalDaHaram
0 Comments