WANE DARASI KA/KIKA ƊAUKA A CIKIN WANNAN TARIHI?
Wata rana Imam Malik bin Anas (93 - 179 AH) رحمه الله yana koyar da almajiransa hadisi a Masallacin Madina, idan ya kawo hadisi, zai kawo isnadinsa baki ɗaya.
Ana cikin karatu, sai ya hango wani yaro yana wasa da tsinke da yawu (yana dangwalar yawun bakinsa da tsinke). Imam Malik ya ci gaba da bayar da karatu, bai masa magana ba har sai da aka kammala majalisin.
Bayan an ƙare karatu, sai Imam Malik ya tambayi wannan yaron: "kai ko me ya sa kake wasa da kara a lokacin da muke koyar da hadisin Annabinmu ﷺ?"
Sai wannan yaron ya ce, ba wasa yake da wannan tsinken ba, a'a; yana amfani da shi ne kamar alƙalami, yana dangwalo yawun bakinsa (a madadin tawada), yana zana abin da ya ji (na karatun) a tafin hannunsa. Yana yin hakan ne, saboda ba shi da kuɗin siyan alƙalami da takarda.
Imam Malik ya cika da mamaki, sai ya ɗan gwada shi, ya ga ko da gaske yake, a nan kwa yaron ya mayar masa duk hadisan da aka koyar, tare da isnadinsu.
Wannan yaron ba kowa ba ne, face IMAMUSH SHAFI'I رحمه الله (150 - 204AH).
Imam Ash-Shafi'i رحمه الله, babban ɗalibin Imam Malik ne a Madinah, don bai bar Madinah ba yana ɗaukar karatu a wajen Imam Malik har sai da Imam Malik ya rasu a 179 Hijiriyya (790 Miladiyya). An ruwaito Imamush Shafi'i ya haddace Alƙur'ani yana ɗan shekara 7, ya kuma haddace littafin Muwatta na Imam Malik (hadisai 1,720) a kwana 9, yana dan shekara 11. A dabi'arsa, yana da nacin tambaya, musamman in ya fahimci kana da ilimi. Idan kuma kai tsaransa ne a ilimi, zai nemi ku tattauna ku ƙarawa da juna ilimi.
WANE DARASI MUKA ƊAUKA DAGA WANNAN TARIHI?
✍️ Aliyu M. Ahmad
27th Safar, 1444AH
24th, September, 2022CE
#AliyuAsks #AliyuMAhmad #RayuwaDaNazari
0 Comments