Don Allah mu fuskanci REALITY, abin da yake shi ne sunnar Allah, sunnar rayuwa.
Ba wani MIRACLE da za ka jira, kuɗi ba daga sama suke zubowa ba, kana zaune; ko tunanin samun wani aiki, ko gudunmawa daga wani mutum, ko jiran gado, ko Pi,... kawai jiran tsammani, kai dai dare ɗaya kurum za ka yi kuɗi.
Idan ma rayuwar wani 'mawaƙi' ko 'cele' ke burge ka, ɗaukakarsu ba miracle ba ce, a hankali suka samu ɗaukaka. Idan rayuwar wani 'ɗan siyasa' ke burge ka, ka bibiyi tarihin gwagwarmayarsa. Idan rayuwar wani 'babban ma'aikacin gwamnati' ke burge ka, ba a zama DG, ko PS a rana ɗaya. Idan wani 'ɗan kasuwa' ke burge ka, ba a dare ɗaya ya kai matsayin da yake ba.
Gaskiyar lamari, kuɗi nemansu ake, a hankali suke taruwa, daga taro, zuwa sisi, kobo, dari... har ka zama 'thousandaire', zuwa 'millionaire', zuwa 'billionaire', 'trillionaire', 'zillionaire'... BA DARE ƊAYA AKE KUƊI BA. Sa gaggawa sai an yi kuɗi ke jefa mutum hanyoyin ya ki halal, ya ki haram.
Duk wanda ya kwanta/zauna yana jiran tsammani, da sunan arziƙi na Allah ne, haƙiƙa ya yi wa Ubangiji mummunan zato ne. Ko tsuntsu da ake kwatantan 'tawakkali' da shi, kullum sai ya fita nema, wannan shi ne sunnar rayuwa. KA NEMA, ALLAH ZAI TAIMAKE KA!
✍️ Aliyu M. Ahmad
14th Safar, 1444AH
11th September, 2022CE
#AliyuMAhmad #RayuwaDaNazari #HalalDaHaram
0 Comments