Kai Ne A Media, Kai Ne A Zahiri

 


Kai! Kada ka yaudari kanka, kana shaƙiyanci, ƙirƙirar labaran ƙarya, batsa da sunan barkwanci ko raha a 'media', ka ce ai a zahiri ba haka kake ba. Da ƙarya da batsar zahiri da ta media, duk ɗaya ce.


Social media is a channel of self-expression. Akwai 'personality theories' da yawa da ake (iya) karanta mutum. Misali, a Freudian Theory (1897), wani yana tsoro ko jin kunyar furta wani abu a zahiri, amma ta media ya samu 'channel' da dama ta wallafa tunaninsa.

A lokacin da mutum ke furucin magana, ko rubutu, yana fitar da abun da ke cikin tunaninsa ne. Wuraren cikin kwakwalwa, Broca na aiki tare da gaɓɓan furuci, domin furuci don isar da sakon ('productive': magana da rubutu). Idan waɗannan wuraren suka sami matsala, shi ne mutum ke gamuwa da 'speech disorder' kamar 'aphasia', ko ta Wernicke a samu 'acoustic neuroma' wajen jin sauti.

Ma'aunin laifi a social media, zai iya ninka na zahiri, saboda, idan ka yi ƙarya ko batsa a cikin ɗaki, tare da abokanka 3, iya abokanka 3 ne za su ji; a lahira akwai shaidu mutum 3 da za su tabbatar ka yi ƙarya. Amma media mutum nawa ne suke following ɗinka, za su bada shaida a kanka a lahira, shi ya sa aka haramta 'mujahara' [Muslim, 2990].

Ai kamar mai ƙiran sallah ne, Abu Sa'id Alkhudry رضي الله عنه ya ce, Manzon Allah ﷺ Ya ce: "فأذنت بالصلاة فارفع صوتك بالنداء ، فإنه لا يسمع مدى صوت المؤذن جن ولا إنس ولا شيء إلا شهد له يوم القيامة" Ma'ana: "...ka yi ƙiran sallah, ka ɗaga muryarka, domin ba wani aljani, ko mutum ko wani abu da zai ji muryarka, face ya bada shaida a ranar Alƙiyama". [Bukhari, 582].

Mu'awiyya bin Haydah رضي الله عنه ya ce, Manzon Allah ﷺ Ya ce: "Narkon azaba ya tabbata ga wanda yake kirkirar karya don ya bawa mutane dariya" [Tirmidhi, 2315]. A wani hadisin kuma, sauran gaɓɓan jiki na zina, zinar harshe shi ne furuci (alƙalami, rubutu) [Bukhari, 5889].

✍️ Aliyu M. Ahmad
8th Safar, 1444AH
5th September, 2022CE

#AliyuMAhmad
#RayuwaDaNazari

Post a Comment

0 Comments