Taimakawa Maɓarnaci a Media

 


Don Allah mu fahimta ⚠️


Idan mutum 1 yana taɓara, ka kawo sunansa 'media', promotion ɗinsa kake (ka sani, ko ba ka sani ba), ba nasiha kake masa ba, don ba ma lalle saƙonka ya isa gare shi ba.

Idan yana da media handle, misali, Reels, Tiktok ko Youtube, a lokacin 'followers/subscribers' da watching time nasa za su karu, domin cikin followers ɗinka, (wasu) za su so su bibiya don ganewa idonsu "contents" ɗinsa.

Me hakan ke nufi? "Monetization earning" ɗinsa zai ƙaru, duk wata akwai kuɗin da ake biyan wanda ya kai wani mataki, na tara followers, subscribers da watching time. Da wannan kuɗin zai sa yi babbar waya, da kayan aiki, ya gyara location, ya ci gaba da harka.

Kai ma ka bada gudunmawar tallata shi. Don ba nasiha ka yi ba. Nasihar taka ba ta je gare shi ba, ka tallata shi, ka kara masa followers, da engagements... Ubangiji kuma Ya ce: "فذكر إن نفعت الذكرى" Ma'ana, "ka tunasar, idan tunasarwa za ta yi amfani" [Al'ala, aya ta 9]. A wata ayar kuma, Ubangiji Ya hana yayata barna, sai in akwai cutarwa ko haƙƙi [An-Nasa'i, aya ta 148].

An excerpt from: WASIƘA GA MAI KALLON BAT*A.

✍️Aliyu M. Ahmad
8th Safar, 1444AH
5th September, 2022CE

#AliyuMAhmad
#RayuwaDaNazari
#FasaharZamani

Post a Comment

0 Comments