Baiwar Sauraro


Sauraro (listening) baiwa ne, don yana da bambanci da 'ji' (hearing). Ji shi ne jin (kowanne irin) sauti ta gaɓɓan ji (auditory organs). Sauraro kuma shi ne jin sautin magana ko ƙara da nufin fahimtar saƙon da sautin ke ƙoƙarin isarwa gare ka a muhallin sadarwa.  Baiwar sauraro tana daga cikin abin da ke bambata ɗan Adam da dabbobi, kuma take bambata zurfin tunanin mutane.

Wanda ya fi ka baiwar 'sauraro' zai fi hazaƙa hatta a wajen gane karatu, ko magana, da zurfin tunani, dalilin kenan da ya sa a ake koyar da 'Listening Skill' ga ɗaliban ajin farko a manyan makarantu, ko; idan malami na koyarwa a aji ke faɗawa dalibai: "listen attentively" domin a fahimci karatu da kyau.

Wannan ya sa ko a cikin Alƙur'ani, Al-Araf, aya ta 204, Ubangiji ﷻ ke cewa: "وإذا قرئ القرآن فاستمعوا له وأنصتوا لعلكم ترحمون". Ma'ana: "Idan ana karanta Alƙur'ani, ku saurara, ku yi shiru, wataƙila a yi muku rahama", ma'ana idan kuka yi tadabburin kalmominsa, kuka yi aiki da su, kwa sami tsira duniya da lahira. 

A hadisin Usamah ibn Sharik (Abu Dawud, 3855) yana kwatanta yadda Sahabai in sun zauna a gaban Annabi ﷺ suna sauraro bayanai, kai ka ce tsuntsun ne a saman kansu saboda nutsuwa da bada hankali a wajen sauraro, da haka suka mana dakon Alƙur'ani Mai girma da hadisan Annabi ﷺ.

A wajen hira, mutane sun kasu kaso biyu, akwai masu sauraron magana don fahimta (listen to comprehend), akwai masu sauraro don maida martani (listen to reply). A ɗabi'a, mata sun fi yawa a rukuni na farko, saboda mace takan saurarawa mai magana, har ya gama, kafin ta mayar (👉bit.ly/3RuoEXL), ba kamar maza ba, shi ya sa da wuya mace ta mance magana, tsawon lokaci.

Idan kana son zama mai buɗaɗɗen ƙirji (open mind), ka koyi dabi'ar sauraro a duk lokacin da wani ke magana, ko ƙoƙarin bayyana abin da ke ransa. Da sauraro Aljannu suka karɓi addinin Musulunci [Al-Jinn 72: 1 - 4]. Da rashin sauraro na fahimta, idan ana jayayya a magana take ƙin ƙarewa, kowa ƙoƙarinsa nasa, ba fahimtar ɗan uwansa ba. Dalai Lama ke cewa: "idan kana furta magana, kana maimaita abin da ka sani ne, amma da za ka saurara, wataƙila ka ɗauki sabon ilimi".

✍️Aliyu M. Ahmad
4th Safar, 1444AH
1st September, 2022CE

#AliyuMAhmad
#RayuwaDaNazari
#FasaharZamani

Post a Comment

0 Comments