Ina kyautata wa masu yin salati ga Annabi ﷺ a 'media' zato, na nuna soyayya ce gare Shi ﷺ. Nuna Soyayya ga Annabi ﷺ ko tunasarwa kan yi masa salati, ibada ce.
Duk wanda ya yi wa Manzon Allah ﷺ salati sanadiyyar tunasarwarka za ka sami lada, gwargwadon niyyarka. Idan ka yi don Allah, don nuna soyayya, ko tunasarwa, za ka samu lada. Idan ka yi da niyyar samun LIKES ko FOLLOWERS, sakamakonka yana ga abin da ka yi niyya, kuma ya zama RIYA da ISGILANCI, don MANZON ALLAH ﷺ BA ABIN WASA BA NE.
Kuskure ne wani shafi kamar na BBC Hausa su yi 'posting' kan wata ƙadiyya da ta shafi labaran ƙasa ko siyasa, ko lafiyar mata ko 'yan film, idan ka duba 'comments:, za ka ga wasu na amfani da kalmomi marasa kyau (zagi ko habaici ko isgili), amma sai ka ga wasu na sa sunan Annabi ﷺ a tsakanin ƙazaman kalmomi, me ya sa ba za ka je shafinka ba?
Wasu kuma za su rubuta salatin ﷺ, su ɗora a shafinsu, ko a status, ko su turo ma ta (Whatsapp) inbox, sai su haɗa da cewa, idan ba ka yi LIKES ko COMMENTS, ko SHARING ma wasu ba, kai munafuki ne, ko wani abu daban, ta ya hakan ya zama ma'auni? Gaskiya mu dawo hayyacinmu, ANNABI ﷺ FI ƘARFIN WASA.
Idan kana ƙaunar Annabi ﷺ da gaske, ka nemi wuri da zauna, ko a tafe, ko kana cikin aiki, ka yi ta masa ﷺ salati cikin ranka, a nutse [Al-A'raf, 7:205]. Manzon Allah ﷺ Yana cewa: "Ku yawaita salati a gare ni a ranar Juma'a da daren Juma'a, duk wanda ya min salati ɗaya, Ubangiji zai yi masa ninkinsa goma (10)" [Baihaqi, 5994].
اللهم صل وسلم على نبينا محمد وعلى آله وصحبه وسلم
✍️ Aliyu M. Ahmad
5th Safar, 1444AH
2nd September, 2022CE
#AliyuMAhmad
#RayuwaDaNazari
0 Comments