Zamani da Media


A wannan zamani ne, abu ne mai wahala, hana 'ya'ya amfani da sabuwar fasaha, ba shi ba ne mafita, saboda gudun lalacewar da ke ciki. Media ta zama tamkar wani sashe na rayuwar duk mai rayuwa a wannan ƙarnin. A nan gaba ma a makarantu, zai zama dole ne a sa darussan digital literacy.

Duk wannan, yana cikin Fiƙhun Imam Aliyu رضي الله عنه cewa:

"لا تربوا أولادكم كما رباكم أباؤكم فقد خلقوا لزمان غير زمانكم."

Ma'ana: "Kada ku yi renon 'ya'yanku kamar yadda iyayenku suka rene ku, domin an halicce su ne a wani zamani ba irin naku ba"  (Ighathat Al-lahfan 2/265)

Media fa kamar duniya ce, akwai wuraren alheri, akwai na sharri, sai inda mutum ya kai kansa, babu abin da babu. Kuma ana zama 'addiction' da media, kamar yadda ake 'addiction' da 'drug abuse', wannan yana taɓa hazaƙar mutum, kazar-kazar da sa lalaci, gurɓata tunani.. Iyaye da masu bayar da tarbiyya ya kamata su fahimci zamanin da ake ciki, domin 'adjusting' na bayar da tarbiyya daidai da zamani. 

A Musulunci, ba abin da ya canja, na haramci da halacci, a kowanne hali, a zahiri, ko a media, misali: kallo batsa, ko bibiyar shafukan taɓararru, mujahara (bayyana laifi), misali, rawar 'yan mata, tabarruj (ɗora hoto da matsattsun kaya, ba lulluɓi) fitana ne, yaɗa labaran ƙarya (fake news), gulma, annamimanci, ƙazafi, rashin kunya wa manya ko cin zarafin mata, jin daɗin hira da ajnabiyya, ha'inci da zamba (fraud), yaɗa ɓarna... DUK FITINA NE, HARAMUN NE.

Su Turawa da yake suna da tsari, kamar Amurka, suna da Children's Online Privacy Protection Act (COPPA). Yaro zai yi amfani da media, amma bai isa ya accessing shafukan da ake wallafa batsa ba, a rubutu, video, sauti ko game, saboda akwai 'age restriction'.

Yau in ana son fesawa mutane wani sabon tunanin, ko sarrafa tunaninsu, da media ake amfani. Ita kwa ɗiya mace, kar ka bari sai saurayi ne zai siya mata waya, yana sa mata kati da data. Akwai waɗanda a zahiri mutanen kirki ne, amma ta inbox da browse histories, suna saɓawa Ubangiji, kamar dai "reaction formation" na Freudian Theory of Personality.

----------------------------------
Rubutu mai alaƙa 👉 https://bit.ly/3PZ2EmB
----------------------------------

✍️Aliyu M. Ahmad
3rd Safar, 1444AH
31st August, 2022CE

#AliyuMAhmad #FasaharZamani #RayuwaDaNazari

Post a Comment

0 Comments