Amfanin Karatu

 


Read, read..!


Kada waɗannan kalmomi su sa ka ji kamar kai ba mutum ba ne, saboda mutane na yawan ɗorawa a media, karatu, karatu... ana ta bada labarin littafai, kai kuma harkokin rayuwa sun ma yawa, ba ka samun damar taɓa takarda.

Kar kalmomin bibliophile, bookworm, reader, booklover... ka ji su kamar wasu mutane ne na daban, kai ma mutum ne. Amfani tara littatafai, sanin littatafai, a karanta, a fahimta. Amfanin karatu kuma, aiki da shi; wataƙila dalilan da su hanaka zama ka buɗe littafi, sune shawarar da ake bayarwa (kenan) cikin littafan. Tara littafi, ba karatu, hoto kenan!

Karatu abu mai kyau, kwakwalenmu na buƙatar sabon ilimi, kamar yadda jikinmu ke buƙatar abinci. Idan har za ka iya samun 10mins, 20mins, 30mins, 1hr...karanta wani ilimi na duniyarka ko lahirarka.

Idan ba ka samun damar yin karatu, ka nemi ɗaya hanyar sa wa kanka sabon ilimi (receptive), SAURARO (👉bit.ly/3QiZmLh) a podcast, ko sautin (mp3) na wani masani. A kowacce rana ka karanta ko ka saurari wani ilimi, da kanka za ka ga rayuwarka, tunaninka da yanayin mu'amalarka yana canjawa.

-------------------------------
Rubutu mai alaka 👉bit.ly/3qdrgha
-------------------------------

✍️Aliyu M. Ahmad
8th Safar, 1444AH
5th September, 2022CE

#AliyuMAhmad
#RayuwaDaNazari
#Karatu #Littafi

Post a Comment

0 Comments