Kowa Ya Tsaya Matsayinsa a Ilimi


 

Da za mu bi ƙa'idar nan ta faɗin Allah (SWT) a cikin Alqur'ani Mai girma da mun huta "ولا تقف ما ليس لك به علم" (Al-Isra, aya ta 36). Kowa ya tsaya matsayinsa a ilimi, ya labarta iya abin da ya sani...


1. Kar ka yi maganar ilimi a kan abin da baka da ilimi, bai iyakance a iya magana kan ilimin addini ba [Tafseer as-Sa‘di p. 457].

Idan kana da ilimin addini, baka da na kimiyya, kar yi kutse cikin ilimin kimiyya. Idan kana da ilimin kimiyya, ba ka da na addini, kar ka yi kutse cikin ilimin addini. Haka, idan baka da ilimi a kan wata mas'ala da shafi siyasa, hukunci, fasaha, falsafa, tarihi da adabi; to kawai ka yi shiru, kada ka tauna.

2. A magana, labari afkuwar wani abu, idan ba ka ji ba, ba ka gani ba, kar ka labarta [Ibn Katheer 5/75].

3. Kowanne dan Adam, mai ilimi, yana da iyakar abin da ya sani na ilimi, yana da ɓangaren da ya fi ƙarfi, akwai kuma inda yake da rauni, babu masanin komai da kowa sai Allah [At-Tahrir wa at-Tanwir
27/269].

Ba dole sai ka san komai-da-komai ba. Mai ilimi shi ne wanda ya kware a wani fanni da in ana neman masanin fannin zai bigi ƙirji, sannan in ya yi magana cikinsa, a gamsu.

4. Ba aibu ba ne don ba ka da wani ilimi. Idan aka ma tambaya kan abun da ba ka da masaniyya, a ilmin addini, ko na duniya, ko da a ɓangarenka ne, ka ce BAN SANI BA, Abu Darda' رضي الله عنه na cewa: "لا أدرى نصف العلم", ma'ana: "(faɗin) ban sani ba, rabin ilimi ce" [Siyar A'lam An-Nubala', 4/318].

An ruwaita cewa, wata rana wani mutum ya zo wajen Imam Malik bin Anas رحمه الله, ya masa tambayoyi kan mas'alolin addini guda 40, Imam Malik ya amsa guda 4, ya ce bai san amsar sauran 36 ba. Imam Malik fa, mai madhba guda fiƙhun addinin Musulunci. Ina ga ni, ko kai?

Na kan tuna malamina a 'Legal' (JSCILS) Auwal Gumel esq., ya kan ce mana, "try to know something in everything, but no matter how hard you push, you cant know everything. Don't be jack of all trades master of none."

Ba kowacce 'saga' ce in ta taso a media za ka yi magana a kai ba ta fuskar ilimi. Mai makon ka nunawa mutane kai wayayye ne, mai ilimi; sai ka je ka yaye hijabin 'jahincinka' saboda yawan son yin magana kan komai da komai.

✍️ Aliyu M. Ahmad
7th Safar, 1444AH
4th September, 2022CE

#AliyuMAhmad
#RayuwaDaNazari

Post a Comment

0 Comments