Media na nufin, traditional media (jarida, mujalla, gidan radiyo/talabijin) ko modern/social media (blogs, social networking [Facebook, Twitter…], video sharing [Youtube]). Dukkan su hanyoyi ne na sadar da saƙo.
Kalmar ‘YAN MEDIA kuma, mun fi danganta ta ga yaran gidan siyasa, masu tallafawa iyayen gidansu a kafafen sadarwar zamani (social media) da yake siyasa yau tana farawa ne daga media. Aikin media ma ‘yan siyasa hanya ce ta samun kuɗi sosai (sana’a ce), amma tana da tsari.
‘Yan media kashi biyu ne, akwai na sa-kai (volunteer) akwai na haya (hired/employed), ya kamata ka san matsayinka, da rukunin ka ke.
Hired social media aides su ne rukunin ‘yan media ne da ɗan siyasa da kansa ke ɗaukar su aiki yana biyansu, saboda yana daga cikin tsare-tsaren neman ƙuri’a (campaing strategy and planning), sune ake cewa NEW MEDIA AIDES, kamar The Buhari New Media Centre (BNMC) a 2015 da 2019, kamar Mustapha Danshatu, wannan rukuni ne na kwararru, lauyoyi, ‘yan jarida, ‘yan gwagwarmaya... A cikinsu, akan samu wanda ɗan siyasa zai riƙa a matsayin Special Assistant (S.A.) on New Media/media aide bayan an ci zabe, kamar su Bashir Ahmad, Femi Adesina da Garba Shehu , Abban Hajia... Akwai kuma waɗanda aikinsu dama kwangila ce ta lokaci (a lokacin yaƙin zaɓe), kuma ɗan siyasar ya san da zamansu, kamar Atiku Kawai Media Group, Media team na Let's Get Nigeria Working Again, su ma suna da alfarma ko bayan an ci zaɓe.
Su kuma ‘Yan volunteer, mutane ne da suka kafa ƙungiya (a kashin kansu) don tallata wani ɗan takara a media (mis. Vanguard, Alliance, Movement, Media Support..). A ƙa’ida ire-iren waɗannan ba biyansu ake ba, sai dai ba su tallafin siyan na data, alawus/kwangila (idan suna da Influencing), ko in za a je yawon campaign ya ɗora su a mota, a ba su kuɗin abinci, in an yi sa’a, a ba su na kashewa (alawus) bayan an dawo. Misalin wannan akwai #IStandwithBuhari, Atiku Kawai, Youth Alliance for Tinubu - YAT da sauransu.
Idan ‘volunteer’ kake a media, to ka tabbatar wanda kake yiwa bauta ya san da zamanka. Ka kasance kana da tsari (strategy and plan) a rubuce, a ƙungiyance/team (ba kai kaɗai ba), ya kasance kana da wata kwarewa da ilimi, kuma kana da sana’a.
Dalilin da ya sa na kawo wannan kashe-kashen a farko, ya kamata ka san matsayin da kake a media. Don da yawa suna ‘claiming’ su ‘yan media gidan wane ne (a siyasa), amma wanen bai ma san da su ba. Ko kuma bayan zaɓe suna kumfar bakin sun yi wa siyasar wani wahala, ya watsar da su. Abin tambayar shi ne, you are hired or volunteered? Don’t depress yourself!
Duk yadda ka kai ga neman wurin zama a wajen ɗan siyasa, kar ka ce za ka masa bauta kai kaɗai, ka je a ƙungiyance, duk influencing ɗin ka (wane ne influencer? 👉 bit.ly/WaneNeInfluencer), ka duba misalin ‘yan 13x13 Movement, da Tinubu Northern Women Support Group da sauransu. Yana daga cikin dalilan da (wasu) ‘yan media siyasa suke kukan cewa an ɗaukaki wani duk da sun fi shi wahala. Influencer yana da tasiri da matsayi na musamma, zai yi posting a rana ya samu likes da comments 500 - 1000+ (misali, Dahiru Mukhtar ), amma wani ɗan media sai ya yi posting bai fi ya samu ‘reactions’ 20, 50+ ba, duba misalan Datti Assalafy ko Rabiu Biyora ko Muhammad T. Shehu.
Idan kana da ilimi da wata kwarewa, da wannan za ka tallata kanka ga ‘yan siyasa cewa, za ka tallafawa tafiyarsa da kwarewarka, misali, marubuci, lauya, social media influencer, malamin addini.... Idan kana da sana’a, ba zai yi zaton ka zo maula ba, kuma ko kwangila za a bada, mai sana’a ake bawa na abin da ya danganci sana'arsa, haka tallafin bunƙasa sana’a.
Ta fuskar zamantakewa da addini kuma:
Da yawanmu muna biyewa 'yan siyasa ne, domin maslahar kanmu, don mu samu rufin asiri. Ma'ana, in an kai ga nasara, a yi gwamnati da mu, mu yi gidaje da abin hawa. Ina da tabbaci, 'yan siyasar nan da ace ba su da wani madafun iko, ko hasashen za su samu, da ko wurinsu ba za mu je ba.
A matsayinmu na Musulmi, MU YI SANI, arziki; Allah ke bada shi, ɗan Adam kawai sanadi ne, tamkar yadda ka yi imani, Allah shi ne ya halicce ka, amma ya yi sanadin zuwanka ta tatson mahaifanka. MUSULUNCI yana nan da tsarinsa, KAR KA RUƊU DA CEWA SIYASA BA ADDINI BA CE, wallahi! A cikin kowanne hali da yanayi, duk abin da ka aikata mai kyau, ko mai muni, da dukkan gaɓɓan jikinka, ko da tunaninka, na mu'amala ko aiki, kai hatta abin da kake ƙullawa cikin zuciyarka, sai an maka hisabi a kansa [Al-Isra', aya ta 37]. Haramun ne ka iya ubangidanka biyayya kan abin da ya kasance saɓon Allah ne "لا طاعة لمخلوق في معصية الخالق".
Don neman wajen zama a wajen ɗan siyasa, kar ka rike ƙarya, ƙazafi, gulma, cin mutunci, ko har ta kai ka ga sihiri (tsafi) ko kisan kai… sune abubuwan neman kuɗi a wajen ɗan siyasa. Mun dai san ‘yan siyasan nan suna da ‘ya’ya da ƙanne, me ya sa ‘ya’yansu ba sa hawa media ana cacar baki ko cin mutunci wani da su? Me ya sa ba sa fitowa su kare iyayen da suka haife su? Kai ka fi su son iyayensu ne? Idan ma ka shiga fadan 'yan siyasa za ka ji kunya.
Don wani ba ya ra’ayin maigidanka a siyasa, ba ya nufin abokin gabarka ne. Za ka iya tallata mai gidanka ba tare da ka ci mutuncin kowa ba. Kar soyayyarka ko goyon bayanka ga dan siyasa ta sa ka zubda mutuncinka, ko ka ɓata alaƙarka da kowa, ko ka yiwa wanda baka ƙauna ƙazafi, ƙarya, habaici da yarfe, ko yaɗa labaran ƙarya (fake news), ko don ruɗarwa ko tabbatar da abin da kake so (confirmation bias), ko rusa abin da baka so (disinformation). Ko abin arziki ne ya zo, offer (ta guraren aiki), ko kwagila, za a yi wa waɗanda suka yiwa siyasa bauta, nutsattsu, masu ilimi da kamala ne ke cin gajiya.
A yi siyasa da ilimi, manufa da tsarari.
✍️ Aliyu M. Ahmad
15th Muharram, 1444AH
13th August, 2022CE
#AliyuMAhmad #RayuwaDaNazari #Siyasa #DanMedia
0 Comments