'Yan Candy


Bayan taya ku murna da fatan alheri, akwai shawara da ankararwar da nake son yi muku (O’Level Graduates).

Mun sani, burin wanda ya kammala karatun sakandire shi ne, ya ci gaba da karatu a matakin digiri (a jami'a), ko wanin haka (college, poly/monotechnic..). Amma a halin yanzu, kusan akwai yayyenku har rukuni 1, a wasu wuraren ma 2 (2020/2021 set[s]) da suke jiran guraben karatu a jami’a? Idan kuwa haka ne, wanda ya yi WAEC da NECO a bana (2022) zai yi jiran kusan shekara 1 ko 2 kenan a gida kafin samun gurbin karatu a manyan makaratun gwamnati. 

Ba ma wannan ba, a halin yanzu ana tsaka da yajin aiki (strike), makaratu da yawa har yanzu suna 2020 Academic Session, wasu ma a 1st semester 2020 Academic Session suke. Wa ma ya san lokacin da za a daidaita tsakanin Federal Government da ASUU har a koma makaranta? Wanda suke ciki ma an jinkirta musu, balle wanda bai shiga ba.

MAIMAKON WANNAN DOGON JIRAN, ba abin da ya kamace ku ‘yan candyn bana, irin ku yi ƙoƙarin koyan wani skills da za ku fara tunanin gina kanku. Akwai skills kala-kala, musamman ga ɓangare computer. Ga maza, akwai tailoring, crafts, welding, bricklaying, mechanic, plumbing, carpentry, yaron kasuwa... Ga mata, akwai tailoring, makeup (MUA), hairdressing, pastries… ga sana'o'i nan da skills da dama.

Ita sana’a, amfaninta ba iya samun kuɗin ba ce, a'a; takan ƙara buɗa mana kwakwale, dogaro da kai, ƙara fahimtar da mu mu’amala da mutane, da kuma karantar da mu ƙalubalen rayuwar duniya na yau da kullum. IYAYE DA YAYYE SUNE ZA SU YI WA ƳAƳA DA ƘANNENSU WANNAN GATAN, maimakon zaman jira, a kai ƴaƴa da ƙanne wajen koyon sana'a, ko makarantun Islamiyya (don koyon addini).

✍️ Aliyu M. Ahmad
12th Muharram, 1444AH
10th August, 2022CE

#AliyuMAhmad #RayuwaDaNazari #Sanaa #Skills

Post a Comment

0 Comments