Bashi



Fassarawa: Aliyu M. Ahmad 

Kai ne abokinka ya ari kuɗinka ₦4,000,000 (miliyan 4) a wajenka tun shekarar da ta gabata, bai biya ka ba, har hakan ya jawo muku matsala a abotarku.

Ka yi ta roƙonsa a ba ka ma iya ₦2,000,000 (miliyan 2) a bar sauran saboda ka shiga matsalar kuɗi, amma sai ya ce abin da zai iya baka ₦1,500,000 (miliyan 1 da rabi) ne, saboda iya abin da yake da shi kenan (a yanzu).

Ka ji, baka da zaɓi face ka amice a hakan, ka tura masa account number don ya tura ma.

Kana tashi da safe, sai ka ga saƙon shigowar ₦15,000,000 (miliyan goma sha biyar), ka tashi ka sake dubawa da kyau, ka tabbatar ₦15m ce.

Kana sake duba wayarka sai ka ƙiran waya (missed calls) 53, da sakwanni (SMS) guda 27, wannan abokin naka na roƙonka ka dawo masa da ₦13,500,000 saboda niyyarsa ya turo ma ₦1,500,000 ya yi kuskuren kara 0.

Idan kai ne wannam mutumin (mai bayar da bashin) wanne mataki ya kamata ka dauka?

1. Za ka maida masa ₦13,500,000
2. Za ka dauki ₦4,000,000 ka maida masa sauran
3. Za ka bar ₦15,000,000 a wajenka
4. Za ka kashe wayarka, ka yi tafiyarka

--------------------------
Nazari! 👇👇👇
--------------------------

Daya daga cikin abubuwan dake durƙusar da ƙananan 'yan kasuwa a farkon fari (start-up) shi ne; (wasu) 'yan uwa da abokan.

Maimakon idan ɗan uwanka ko abokinka ya fara kasuwanci, ka jibance (patronizing) shi, ka riƙa siyan kaya a wajensa, jawo masa customers (referral); sai ka maida shi saniyar tatsa, an samu wajen cin kaya a banza (kyauta), neman mummunan ragi (bad discount), ko a durƙusar da shi da karbar bashi. 

1. Idan ka karɓi bashi a wajen ɗan kasuwa na 20k har ka wuce sati, ba wai illar rashin dawo masa da shi kadai ka masa ba; da a ce 20k din nan a hannunsa take, cikin sati zai iya juya ta ta zama 23k, 25k ko ma fiye da haka. 

2. Idan ka karɓi bashi dan kasuwa, ko baka biya shi bashin ba, ka ci gaba da zuwa kana jibartar (patronizing) na siyan kayansa. Amma wasu da yawa za su karɓi bashin ɗan kasuwa, ba su biya ba, kuma su daina harka siyayya da shi, su koma wani wajen. Kisa 2 kenan, ba biyan bashi, ba cinikiyya.

3. Idan ka karɓi kaya a wajen mai siyarwa, kai baka biya ba, kuma kai baka ce bashi ka karɓa ba; ka sani wannan aikin naka 'riba ne'. Kuma mun san matsayin 'riba' a addinin Musulunci. 

Alaƙa irin wannan, tana kashe ƙananan har da ma manyan 'yan kasuwa da yawa. Kuma dama ya kama shi ma mai sana'a ya san hannunsa da kyau, ta yadda kar ya bari alaƙar zumunci ta rusa masa mafarkinsa, ya kuma iya mu'amalar da kyautatawa daidai gwargwado da ba zata ɓata masa zumuncinsa da 'yan uwa da abokan arziki ba. 

✍️ Aliyu M. Ahmad
20th Rajab, 1443AH
22nd February, 2022CE.

#AliyuMAhmad #RayuwaDaNazari #Sanaa #Nazari


Post a Comment

0 Comments