Facebook Friend(s)


Don Allah mu fahimci wannan! Ba sai lalle mun zama 'friends' ba za mu rinƙa mu'amala a Facebook ba, za mu iya zama followers.

Friend a Facebook shi ne wanda yake cikin friendlist mai wurin mutane 5000. Kai tsaye, duk wanda kuka zama 'friends' a Facebook kun zama followers ga juna (mutual). Follower shi ne mai bibiyar duk abin da ka yi posting a 'wall/timeline'. Banbancin 'friend' da 'follower' a posting (kawai) 'mutuality' ne, sai wajen 'tagging', ko samun wasu bayanai da aka iyakance ga 'friends only'.

Mu fahimta! Duk waɗanda friends nasu suka cika 5000, ba su da damar ƙara karɓar 'friend requests', duk wanda ya turo musu 'friend request' za su zama cikin followers (masu bibiya) ne kai tsaye. 

Haka shi ma wanda friends nasa suka cika 5000, in ya tura wa wani 'friend request', ba za a iya karɓar 'friend request' nasa ba, sai dai ya zama 'follower' shi ma 

Ba wani abu ba ne idan ka zama follower, kusan ɗaya ne da mutual friendship, shi ma 'friend 'ɗin 'follower' ne (mutual). Yadda 'friend: zai ga 'posting', ya yi 'liking', da 'comments' da 'sharing' na posting ɗin wanda kake following, kai ma haka za ka gani, ka kuma iya yin 'reactions', sai dai idan ya yi limiting (friends only) na wasu features. Kuma za ka iya turawa wanda kake following saƙo ta Messenger, sai dai in ya rufe (friends only). Za ka mentioning na wanda ba ya cikin 'friendlist' naka a kasan wani posting ta hanyar amfani '@', sai ka rubuta sunansa (misali, @Aliyu M. Ahmad).

Kamar ni, ba ni da tsarin in cire wani a friendlist don karɓar wani, akwai mutane da yawa da suna bibiyarka da duk abin da kake, reactions (likes & comments) ne kawai ba sa yi, AND 'AM NOT AFTER THAT. Kuma za su baka kyakkaywan 'review' kan abin da kake ta private (DM/PM), ku ƙarawa juna ilimi.

Mu daina damun kanmu da sai an karɓi friend request namu matuƙar muna iya ganin postings, muna iya reactions, muna iya tura wa juna saƙo.

Allah Ya ba mu ikon amfana da juna.

✍️ Aliyu M. Ahmad
12th Muharram, 1444AH
10th August, 2022CE

#AliyuMAhmad #RayuwaDaNazari #FasaharZamani #Facebook #FacebookFriends

Post a Comment

0 Comments