Telegram
Kamar Whatsapp, Telegram manhajar IM (instant messaging) ce ta wasu ‘yan Russia ne Nikolai Durov da Pavel Durov. An fara buɗe shi a 2013, bayan shekaru 4 da fara Whatsapp na Brian Acton (American) da Jan Koum (Russian).
Telegram yana da tsari irin na Whatsapp, ana amfani da lambar waya wajen buɗe shi, kai! kamar ma ya fi Whatsapp (wasu) features da yawa, in ka cire yin ‘Whatsapp status’.
1. Telegram Cloud based IM ne, baka buƙatar yin backup na messages, saboda a kowanne lokaci ka canja waya, chats da files suna nan. Ko a group aka saka ka, za ka iya scrolling na files da chats da aka turo kafin shigarka group ko channel.
2. A Telegram ana iya tura file da ya kai nauyin 2GB. Sannan a tura hoto, kana iya zaɓar yin compressing (rage masa nauyi) ko ka tura a yadda yake. Ba kamar a Whatsapp ba, inda idan ka tura hoto a ‘megabytes’ zai maida shi ‘kilobytes’, ya rage masa nauyi da ‘quality’.
3. A Telegram, ana iya 'editing' message da aka tura a ƙasa da awa 48, kuma ana iya goge saƙo (both) a kowanne lokaci, ba kamar a Whatsapp ba, bayan wani lokaci mai tsayi da tura saƙo, ba za ka iya “DELETE FOR EVERY ONE” ba, sai dai “FOR ME”.
4. A Telegram ana iya saita ‘scheduled messages’, idan ka tura saƙo, zai goge kansa da kansa, misali, bayan 1hr, ko 1 day, ko sati, ko wata, gwargwadon yadda aka scheduling.
5. Telegram yana da tsarin ‘secret message’, idan ka saita, ka yi chat da mutum a 'secret chat', ba zai iya screenshot, ko forward zuwa ma wani ba, kuma chat ɗin zai goge bayan ‘timer’ da aka saita ya cika, ba kamar ‘once seen’ ba na Whatsapp.
6. Za ka iya ‘login’ Telegram a devices daban-daban, ba kamar Whatsapp ba, da a iya device ɗaya ne, sai kuma ‘link device’ na desktop’. Za ka iya ‘login’ Telegram a kan computer da lambar waya, ba tare da haska barcode ba.
7. Telegram yana da tsarin ‘draft sync’, ma’ana idan ka fara rubutu a Telegram a wani device ɗin, za ka iya ci gaba da yi a wani, kafin ka tura.
8. Za ka iya haɗa chats ko groups a folder daban-daban.
9. Group a Telegram yana ɗaukar mutum 1 - 200,000 kamar a Whatsapp ba da iya mutane 512 iyaka a group (a yanzu).
10. Channel a Telegram ba kamar na broadcast na Whatsapp ba ne, shi za ka ƙirƙirar shi, mutane su iya join, ko saka su, kuma saura waɗanda suka yi join ba za su ga sauran followers ba, sai admin kawai, kuma dubban nan mutane na iya following, ba iyaka (misali, t.me/aliyumahmad).
11. Ana iya haɗa 'polls' (zaɓe) ko quiz (gasa) mai zaɓi-ka-tika (objectives) a Telegram group, a (kuma) fidda sakamako.
12. Za ka iya exporting/forwarding na file daga Telegram zuwa Whatsapp, da sauran platform a tsari data portability (Whatsapp ma na irin wannan).
13. Za ka iya canja timestamps na last seen da ‘last seen recently”, za ka iya rufe online status a Telegram.
14. Ana voice da video call da Telegram. Ana iya haɗa voice/video chat a group, kamar yadda ake conference call. Admin yana damar muting na member, yana kuma da damar ba wa member damar Magana.
A video conference na Telegram group, mutane 1000 na iya ‘live streams’, za kuma a iya amfani da OBS Studio ko XSplit domin ba wa mutum sama da dubu damar bibiyar live, za kuma ka iya recording na conference a Telegram.
15. Idan ka tura link na downloading file, misali pdf, ko mp3; za ka iya sauke shi kai tsaye daga cikin Telegram ba sai ya ‘pop-up’ a browser ba.
16. A wajen chat (text) ana iya yi wa rubutu bold, italic, underline, strikethrough, mono (font) da spoiler. Za ka iya saita ‘text size’. A Telegram akwai emojis, live emojis, mask, da kuma stickers sama da 20,000 a cikin packs.
17. Ta ɓangare tsaro, Telegram na da factor authentication, za kuma ka iya saita ‘password’ kafin buɗe shi. A privacy kuma, za ka iya saita wanda zai yi ma voice/video call, ko saka ka a group, sannan idan wani ya yi forwarding files, ko chat dinka, sunanka zai fito a kai (mis. from Aliyu M. Ahmad)
18. Idan ka yi wata 6 kana ‘inactive’ (ba ka hau Telegram ba), za su goge ‘user’ ɗinka, amma ana iya saitawa zuwa shekara 1.
• Telegram na Android 👉 bit.ly/3QHRJyS
• Telegram na iPhone/iSO 👉apple.co/3R3zRye
• Desktop 👉 web.telegram.org
✍️ Aliyu M. Ahmad
26th Muharram, 1444AH
24th August, 2022CE
#AliyuMAhmad #FasaharZamani #Telegram
https://bit.ly/3ci0xfW
0 Comments