Dabi'ar Hira


A Dabi'a (2)

Wardaugh Ronald (2002) cikin 'Sociolinguistics' ya kawo nazari kan ɗabi'un mata da maza wajen magana da hirar yau da kullum na Coates (1986):

Idan 'yan uwa nisa'u (mata) na hira a tsakaninsu, yawancin abin da suke tattaunawa, abu ne da ya shafi rayuwar mu'amalarsu ta soyayya ko zaman aure, a karan kansu, ko a kan waninsu (shi ya sa ake ga kamar mata sun fi maza gulma). Su kan ɗaukar lokaci (mai tsayi) suna hira. Kuma a ɗabi'arsu (mata), idan ɗaya tana magana, ɗaya za ta saurara har sai ɗayar ta gama magana, tukun a fara musayar ra'ayi.

A hirar rijalu kuwa, yawancin hirarsu kan abin da ya shafi rayuwar yau da kullum ne, ba su fiye hira rayuwarsu da iyali ko alaƙar soyayya ba a majalissa, sannan kowa so yake ya kasance ya fi kowa baki, abin da ya faɗi shi ne daidai. Shi ya sa idan maza na hira kan kwallo ko siyasa, sai ka zaton kamar faɗa ake, kowa yana faɗar ra'ayinsa da ƙarfi-ƙarfi, so yake a ce shi ne ke faɗar daidai. BA FAƊA BA NE,  ɗabi'a ce, da yanayin hira, kuma za a ci gaba da mu'amala ba tare da wani ya ƙullaci wani ba.

Idan kuma aka haɗu hira tsakanin namiji da mace, ita mace na buƙatar in tana magana, kar a mata katsalandar, har sai ta tuƙe, kullum so take a saurare ta. Shi ya sa, hatta malaman tarbiyya suke ce wa ga ma'aurata, idan matarka na ƙorafi, ka yi shiru ka saurare ta, fitar da maganar dake ƙirjinta shi ne zai rage mata damuwa. 

Shi kuma namiji, in ya faɗi magana, ba ya son a saɓa masa, koda kuskure ya yi, ba ya son yin reverse, wanda wannan a wasu lokutan akan samu kuskure ko cutuwa, musamman a tsakanin 'ya'ya da iyaye, ko daga maza ga matayensu, da sunan mazantaka.

✍️ Aliyu M. Ahmad
24th Muharram, 1444AH
22nd August, 2022CE

#AliyuMAhmad #RayuwaDaNazari #Muamala #Dabia

Post a Comment

0 Comments