Baiwar Harshe 🧠
(Linguistic Intelligence)
Baiwa wata dama ce da Ubangiji ke azurta bayinsa ta kwarewa kan wani fannin rayuwa. Baiwa kala-kala ce, akwai ta ƙirkire-ƙirkire, lissafi, mu'amala, motsa jiki, karatu da koyarwa, sarrafa harshe da sauransu (Gardner, 1983).
Baiwar harshe, dama ce da Ubangiji ke bawa 'yan Adam ta sarrafa harshe wajen isar da saƙo don nishadantarwa, ko faɗakarwa, ko fahimta da adana saƙo (Gardner, 1983). Baiwar harshe ba sai wanda ya karanci harshe (linguistics/languages) ba
Baiwar harshe ba ta taƙaita ga wani harshe ba, misali; Turanci, kamar yadda ake faɗi "Turanci ma'aunin baiwa ne" (English is a measure of an intelligence) ko Larabci da ake ce wa"تعلموا العربية؛ فإنها تثبت العقل" "ku koyi Larabci, domin zai buɗa muku tunani", Chinese ma suna da nasu "學習語言就是多一扇觀察世界的窗口" ma'ana: "koyon yare, hanya ce ta buɗe sabuwar ƙofa da za ka kalli duniya" irin kirarin nan, Hausawa ma na da shi, "Hausa ba dabo ba ce (wani ma in ya isa ya yi)"... kowanne harshe da nasa salon, baiwar ɗaya ce, harshe ne ke bambantawa, "(haka Allah Ya so Ya sanya) mu saɓa a launin fata da harsuna" [Rum, aya ta 22]. Buƙatuwar harshe ke ba shi matsayi wajen amfani, misali, a addini (Larabci), yaren ƙasa (Turanci a Nijeriya, a Nijar Faranci)
Duk mutumin da yake iya magana da harshensa, to; yana da baiwar harshe (don akwai waɗanda ake haifa ma, ba sa iya magana). Sai dai, akwai waɗanda Allah Yake ɗaukakawa da baiwar fiye da sauran mutane, daga ciki akwai masu baiwar harshe ta ɗauka (comprehension: ji da karatu), wasu ta bayarwa (generation: magana da rubutu). Koyon wani yaren ma, baiwa ne. Wani yana da baiwar jin yare biyu (bilingual), wani yaruka da yawa (multilingual).
Akwai mutanen da Allah Ya yi wa baiwar sarrafa harshe don isar da saƙo ta salon furuci a cikin jama'a (public speaking, mis. Sir. Tafawa Balewa da Marigayi Danmasanin Kano, wani ba zai iya tsayawa a gaban mutane ya yi magana ba), koyarwa (mis. Mal. Daurawa) akwai baiwar waƙa (misali, Mamman Shata), akwai karin magana, ƙarangiya, zaurance, barkwanci, ƙirari, habaici.. duk don yi wa harshe ado.
Rubutu ma baiwa ne! Akwai waɗanda Allah Ya yi wa baiwar rubutu, kuma saƙonsu yana isa ta hanyar zube (rubutun labari, waƙe, ko wasan kwaikwayo) ko muƙala (article) don wayarwa da mutane kai.
Da harshe ake koyar da kowanne irin darasi a makarantu (wani yana da ilimi, amma ba shi da baiwar iya bayani), wani yana da baiwar isar da saƙo (masu talla ko 'yan jarida da masu sharhi [commentators]), yarjejjeniya, zaman majalissa a zauren ƙasa, tsara bayani... da harshe mutum ke nuna su, ruwan mutum ne ya yi amfani da baiwarsa wajen shiryar da al'umma, ko neman kuɗi, ko gurɓata al'umma.
Hausa is also a measure of intelligence.
✍️Aliyu M. Ahmad
29th Muharram, 1444AH
27th August, 2022CE
#AliyuMAhmad #RayuwaDaNazari #RanarHausa
0 Comments